A yayin jawabinsa a wajen Mauludin, Jagora ya karanto ƙissar haihuwar Imam Ali (AS) a cikin ɗakin Ka'aba, a rana mai kama ta yau, Juma'a 13 ga watan Rajab, shekara ta 30 bayan haihuwar Manzon Rahma (S).
Ya kuma yi bitan wasu daga darajojin Imam Ali (AS), da yadda Allah Ta'ala Ya fifita shi akan kowa a halittunSa baya ga Manzon Allah Muhammad (S), kama daga Ilimin Amirulmuminin, wanda yace shi ne wanda Allah Ta'ala Ya siffanta shi da "Allazi indahu Ilmul Kitab."
Da yake bayani dangane da Zuhudun Imam Ali (AS), Jagora (H) ya bayyana yadda Imam ke wadatuwa da kansa. Ya kawo kissar cewa: “Shi ne wanda da zai shiga Kufa, ya riƙe ragamar Goɗiyarsa, yace, ya jama'a, kun ganni nan? Kun ga goɗiyata? Kun ga takalmi na? To in kuka ga na canza, to na ci amanarku.” Yace kuma, "Na wadatu da abubuwa guda biyu; tsofaffin riguna guda biyu, da kuma gurasa guda biyu a rana.”
Ya bayar da kissar wani da ya kasa cin abincin Amirulmuminin, sai da Imam Ali (AS) ya tura shi wajen ɗansa Imam Hasan (AS) ya ci abincinsa. Mutumin ya rika mamaki akan yadda Imam Ali (AS) wanda ya kasance shi ne Amirulmuminin, kuma Sarkin Musulmin duk duniya a lokacin, amma ya kasance a gona, kuma ba a iya cin abincinsa saboda tauri. Jagora (H) yace, “Kar mutum yace, to me yasa Imam Hasan (AS) yake cin abinci mai kyau, alhali shi babansa baya cin abinci mai kyau?” Ya amsa da cewa, “Shi babansa ne yace, ni a duniyarku wadannan sun ishe ni. Amma yace, kar ku kwaikwaye ni, don ba za ku iya ba, amma ku tayani da abu guda, kada ku ci haram.”
Yace: "Saboda haka kar kace, to kai kace Imam Ali ya wadatu da tsofaffin riguna guda biyu, amma ka je ka shawo riga mai kyau. Ai ba haramun ba ne. Sai dai kar a samu ta haram. A kuma ci abinci da mai da nama, amma ba daga Haram ba.”
Jagora ya ambaci kissoshi daban-daban na irin jarumtar Amirulmuminin (AS), da sadaukarwarsa, da kuma yadda Allah Ta'ala Ya fifita shi da kasancewa ta hanyarsa da Sayyida Zahra (SA) ne kadai aka samu magada kuma zuriyar Manzon Allah (S).
Ya kuma bayyana muhimancin raya Mauludan A'imma (AS) da raya karantarwarsu. Inda ya bayyana Mauludi da Zikiran Wafatinsu a matsayin hanyar sanar da al'umma su wane ne su, da kuma karantarwarsu. Yace, “Tunatarwar nan da ake yi, yana raya abin ne, domin abubuwa da dama mutane a lokacin Mauludai ne suke saninsu. Wasu basu da imkaniyar su yi karatu, amma za su ji in aka yi musu bayanai daban-daban. Don haka kun ga kenan ta hanyar haka nan ne muke raya lamarin.
Yace, “Al'amarin Ahlulbaiti (AS) yana ta rayuwa, su kuma masu adawa suna ta adawa, kuma basu iya yin komai sai dai adawa. Komai aka yi su yi suka. Mukan ce wadannan mutanen a daina ma daka tasu, mu dinga basu haushi ne ta hanyar yin abinda basu son su gani. Mu dinga raya abinda basu so a raya. Mu dinga faɗin Ali, Ali, Ali, Ali...”
Yace, za ka ga suna ta fushi in ana kiran sunan Imam Ali, kamar su fashe. “Amma wani abu ne zaunanne, Allah Ta'ala Ya ma Imam Ali daraja, baya ga Manzon Allah, ba wanda ya kai Imam Ali daraja... Daraja ce Allah Ya riga ya yi ya aje a nan, kuma in kana son mafita ka bar daraja a inda aka ajiye, ta nan ne kai ma za ka samu daraja din.” ya jaddada.
Jagora ya rufe jawabinsa da jaddada godiya ga Allah Ta'ala da ya sanya mu cikin ma'abota Wilaya. Yace: "Muna rokon Allah Ya tabbatar da mu akan Wiyalar Imam Ali (AS). Ya rayar da mu a Wilaya, ya dauki rayukanmu a Wilaya, ya taso da mu a Wilaya, ya gama mu da waɗanda muka bi, wadanda Yace a bi su. Insha Allah.”
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
13/Rajab/1447
02/01/2026
Your Comment