Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya kawo maku rahoton cewa: an kai hari kan wata makabartar Musulunci a unguwar "Naraylan" a kudu maso yammacin Sydney, Australia, inda aka sanya kawunan aladu da sassan jikinsu da dama a bakin kofar makabartar.
Wannan lamari ya faru ne bayan harin makami da aka kai a bakin tekun Bondi jiya, Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 16.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna cewa an lalata makabartar Musulman. Inda 'Yan sandan Australia suka sanar a cikin wata sanarwa cewa sun sami rahotannin kasancewar gawarwakin dabbobi a bakin makabartar da ke kan titin Richardson da misalin karfe 6 na safe a ranar Litinin.
Bayan isa wurin, jami'an sun gano wasu kawunan aladu kuma nan take suka fara bincike. 'Yan sanda sun jaddada cewa an tattara gawarwakin kuma an zubar da su gurun da ya kamata kuma ana ci gaba da bincike.
A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa Navid Akram, mai shekaru 24, da Sajid Akram, mai shekaru 50, ana zarginsu da hannu a harbin da aka yi a wani cocin Yahudawa a ranar Lahadi. Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin ya haura 16, ciki har da wata yarinya 'yar shekara 10 da wani mutum mai shekaru 40 da ya mutu a asibiti.
A wani jawabi da ya yi a yammacin Lahadi, Kwamishinan 'Yan sandan New South Wales, Mal Lanyon, ya bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar fansa, kuma kada su mayar da hankali kan jita-jitar da ake yadawa ta intanet.
Ya jaddada cewa 'yan sanda suna binciken lamarin da gaske da sauri, kuma ya kamata jama'a su bai wa jami'an tsaro lokaci don yin aikinsu. Ya yi alkawarin cewa za a ci gaba da sanar da jama'a game da binciken.
Your Comment