Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: sabbin bayanai da Babban Bankin Isra'ila ya buga sun ba da rahoton ƙarin raguwar ajiyar kuɗin ƙasashen waje kafin ƙarshen Nuwamba 2025; batu da ya sake jaddada raunin yanayin tattalin arzikin Isra'ila a fuskar rigingmun cikin gida da haɗarin kasuwanci.
A cewar wani rahoto da jaridar Isra'ila "Globes" ta fitar, asusun ajiyar kuɗin ƙasashen waje na Babban Bankin Isra'ila ya ragu zuwa dala biliyan 231.425, wanda ya yi ƙasa da dala miliyan 529 da aka tabbatar a ƙarshen Oktoba. Jaridar ta ƙara da cewa kason ajiyar kuɗin da aka samu ga babban kayan cikin gida na Isra'ila (GDP) ya kasance a kashi 39.7%; kason da ke nuna cewa gwamnatin ta dogara da albarkatun kuɗi na ƙasashen waje wanda ba ya hauhawa da saurin da ake buƙata.
Isra'ila Ta Fara Amfani Da Kuɗaden Da Ta Taskace Mai Yawa
Globes ta bayyana cewa raguwar ta faru ne saboda ayyukan gwamnatin Isra'ila a kasuwar musayar kuɗi ta ƙasashen waje wanda ya kai kimanin dala biliyan 1.075, amma wani ɓangare na sake kimanta kadarorin da suka kai dala miliyan 568 ne kawai aka rage. Ma’ana ci gaban ba sakamakon kwararar kuɗi na gaske ba ne kawai gyara ne na lissafi na ɗan lokaci.
Ko da yake ajiyar Bankin Isra'ila ta ƙaru idan aka kwatanta da ƙarshen Nuwamba 2024, lokacin da suka kai dala biliyan 217.174, Globes ta yi gargaɗin cewa wannan ci gaban shekara-shekara ba alama ce ta lafiyar tattalin arzikin Isra'ila dai-dai ba, musamman idan aka yi la'akari da ci gaba da matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi ta ƙasashen waje da raguwar amincewa da ikon manufofin tattalin arziki na tallafawa shekel.
Kasuwanci Ba Tare Da Tabbaci Ba
Jaridar ta tuna cewa a watan Yunin 2025, Bankin Isra'ila ya tilasta sayar da kusan dala miliyan 300 a musayar kuɗi ta ƙasashen waje; wannan shine kasuwanci na farko tun farkon yakin Gaza, yana nuna cewa shiga wannan kasuwanci ba da san rai ba ne na dole ne cikin gaggawa ne.
Globes ta kuma nuna shawarar Babban Bankin Isra'ila bayan fara yakin Gaza a watan Oktoban 2023, wanda aka tsara zai sayar da dala biliyan 30 don tallafawa shekel, amma a zahiri dala biliyan 8.5 ne kawai aka sayar, mafi yawansu a cikin 'yan makonni kaɗan; batun da ke nuna tsagwaron tasiri da zurfin tabarbarewar.
Your Comment