7 Disamba 2025 - 21:14
Source: ABNA24
Nasarar Fagen Gwagwarmaya Ita Ke Bayyanar Da Hasashen Alqur'ani

Nasarorin da fagen gwagwarmaya ke samu, tun daga fagen gwagwarmayar Yemen wajen fuskantar Amurka, ta sanadin wannan koyarwar ta Alƙur'ani da kuma tsantsar biyayya ga mai waliyil Amr ne.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Hujjatul Islam Khamushi, a bikin rufe gasar Alqur'ani mai tsarki a birnin Qom, Iran, ya taya murnar zagayowar ranar haihuwar Sayyidah Zahra (A.S.), tare da yin nazari kan abubuwan da suke faruwa a yan kwana nan a yankin bisa bisa dogaro a bayaninsa ga ayoyin Allah, sannan ya danganta shan kayen da Isra'ila da Amurka suka sha a yaƙe-yaƙen baya-bayan nan ga samuwar jagorancin Ayatullah Khamenei mai hikima.

Ya jaddada cewa wadannan fadace-fadacen sun yi daidai da hasashen Alqur'ani mai tsarki, musamman Suratul Hashr, inda halayen munafukai na wancan lokacin suka yi kama da munafukai da masu mulkin mallaka na wannan lokacin wadanda suka yi alkawarin nasara ga abokan gaba.

Da yake ambaton ayoyi daga Alqur'ani, shugaban cibiyar bayar da tallafi ya tunatar da makiya game da tsananin tsoron da suke yi wa al'ummar Iran kuma ya tambayi dalilin da yasa mutane kamar Trump ke ci gaba da ambaton sunan Janar Sulaimani, wanda ke nuna karfin tasirin gwagwarmaya.

Ya ɗauki babban tushen Taqawa a wannan fanni a matsayin "taƙawar zamantakewa" kuma ya jaddada buƙatar bin taswirar da Jagoran Juyin Juya Halin ya bayyana a Mataki na Biyu na Juyin Juya Halin.

A ƙarshe, ya danganta nasarorin da fagen gwagwarmaya ke samu, tun daga fagen gwagwarmayar Yemen wajen fuskantar Amurka, ta sanadin wannan koyarwar ta Alƙur'ani da kuma tsantsar biyayya ga mai waliyil Amr.

Ya bayyana fatan dacewa ga wannan fahimtar ta kalmar wahayi ta zama farkon cimma manyan manufofi da kuma shimfida harsashin bayyanar Sahibul Asr (a.s.) da kuma fatan cewa Iran za ta iya jurewa da kuma cin nasara a kan tsarin mulkin mallaka a fannoni daban-daban na tattalin arziki da soja.

................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha