Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBayt (ABNA): Abu Abdurrahman, Hujr ibn Adi ibn Muawiyah Kindi, wanda aka fi sani da "Hujril-Khair (Dutsen Alkhairi)" da "Ibn Adbar" (1), yana ɗaya daga cikin waɗanda suka riski zamanin Jahiliyya da Musulunci (2). Ya shiga wurin Annabi (amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalansa) (3) kuma ya tattauna tare da shi (4).
Hujr yana ɗaya daga cikin fitattun mutane a tarihin Musulunci kuma ɗaya daga cikin fitattun mutane a tarihin Shi'anci.
Tun yana ƙarami lokacin da ya zo gaban Annabin Allah ya rungumi Musulunci. Halayensa da ya shahara da su sun haɗa da gudun duniya, yawan Sallah da azumi, jarumtaka da yaƙi, girmamawa da mutunci, gaskiya da kokarin yin ibada(5).
An san shi da gudun duniya (6). Ruhin Hujr mai tsarki, ruhinsa mai lafiya, halinsa mai kyau da kuma kyawawan halaye su ne suka sa ya zama wanda addu’arsa take karbuwa (7).
Bai taɓa yin shiru ba a fuskar rashin adalci da ƙarya. Don haka, shi, tare da muminai da mayaƙa, suka yi wa Uthman tawaye (8) kuma ba su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ikon Ali (aminci ya tabbata a gare shi) a zahiri, don haka, an ɗauke shi ɗaya daga cikin sahabbai na musamman (9) da mabiyan Imam Ali As masu biyayya (10).
Ya halarci yaƙokin Ali (aminci ya tabbata a gare shi). A yakin Jamal (11), shi ne kwamandan mahaya na rundunar Kindawa (12), a Siffin (13), shi ne kwamanda na ƙabilarsa (14), kuma a Nahrawan, ya jagoranci gefen hagu (15) ko dama (16) na rundunar Imam Ali As.
Yana da harshe mai iya magana da ratsa jiki. Ya yi magana da kyau kuma ya bayyana gaskiya da iya magana. Kalmominsa masu kyau da farkarwa game da babban matsayin Imam Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) alama ce ta wannan gaskiyar (17).
Shi Baban mataimaki ne ga ubangidansa Imam Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) kuma ɗaya daga cikin masu kare shi mai himma. Lokacin da Dahhak ibn Qais ya tafi Iraki don yin fashi da wawashe dukiyar al’umma, Hujr ibn Adi ya sami umarni daga Ali (a.s.) don ya fuskanci shi ya kuma yi hakan ta hanyar cin nasara cikin jarumta har ta kai ga Dahhak ya gudu (18).
'Yan mintuna kafin a sari Imam Ali (a.s.), Hujr ya ji labarin makircin kuma ya yi ƙoƙarin sanar da shi da dukkan ƙarfinsa; amma bai yi nasara ba (19) kuma baƙin cikin zubar da jinin maigidansa (a.s.) ya mamaye shi.
Shi ma yana ɗaya daga cikin sahabbai masu himma da juriya na Imam Hasan (a.s.) (20). Da ya ji labarin sulhu da Imam yayi, jinin kishi ya tafasa a cikin jijiyoyinsa kuma ya nuna rashin amincersa ga wannan Sulhun (21). Imam Hasan (a.s.) ya gaya masa: "Da akwai wasu masu daukaka kamar ku, da ban taɓa sanya hannu kan wannan yarjejeniya ba (22)".
Hujr yana da zuciya cike da kiyayya ga Mu'awiyah kuma koyaushe yana ƙin fuskar "Hizbut Tulqa (gungun da aka 'yantar bayan bude Makka)" waɗanda suka sami iko ya kasance tare da wasu ‘yna shi’a suna la'antar wadannan mutane (23); domin su gungu ne da Annabin Allah ya ɗauke ta a matsayin "la'anannu".
A duk lokacin da Mughirah - wanda ya kasance ba ya da tsara a dukkan munanan ayyuka da ƙazanta da rashin kunya ya sami iko a Kufa da bisa da rashi a kan mulki da "Hizbit-Tulaqa" su kai - ya zagi Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da mabiyansa, Hujr yana tsayawa wajen kare shi ba tare da tsoro ba ya na mai tozarta shi (24).
Mu'awiyah, wanda ya gaji da matsayin da Hujr ya ke dauka ya ba da umarnin kisansa kuma ya shahadantar da shi tare da sahabbansa (25) a "Marj Azra'(26)"(27) a shekara ta 51 AH(28).
Hujr yana da fuska mai farin jini, hali mai ƙarfi da kuma kyakkyawan suna. Shahadarsa ta kasance abu mai nauyi ga mutane (29). Don haka, suka yi zanga-zanga a kan Mu'awiyah suka la'ance shi saboda wannan mummunan aikin. Misali, Imam Husain (amincin Allah ya tabbata a gare shi) (30) a cikin wata wasika da ya rubuta wa Mu'awiyah, yayin da yake yabon Hujr da halayensa na kin jinin zalunci, ya nuna rashin amincewarsa ga Mu'awiyah ya tunantar da shi karya alkawarinsa ta hanyar zubar da jinin Hujr da ba shi laifi a kasa. Aisha ta kuma nuna rashin amincewarta ga Mu'awiyah ta hanyar ambaton wani labari game da shahidan "Marj -Azra" (31) (32).
Duk da duk munanan laifukansa Mu'awiyah ya dauki kisan Hujr a matsayin daya daga cikin kurakuransa kuma ya nuna nadama a kansa (33) kuma ya ce a lokacin mutuwarsa: "Da akwai wani mai ba da shawara ya kasance da ya iya hana mu kashe Hujr" (34).
Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya sanar da shahadarsa kuma ya kwatanta shahadarsa da ta sahabbansa da shahadar "Sahabban Ukhdud" (35) (36).
Your Comment