Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, Ministan Tsaro, ya shaida wa ɗaliban Jami'ar Fasaha ta Malek Ashtar: "Daga ƙasashen yankin zuwa Ukraine, duk inda Amurka ta shiga to zaka ga sakamakon shigar ya kasance matsin lamba, yaƙi, da yaudarar ra'ayoyin jama'a. Kuma a yankin, gwamnatin Sahyoniya kayan aiki ne na aiwatar da manufofin Amurka; wani sansani da Amurka ta ƙirƙira don cimma burinta na kama-karya a yankin.
Ƙasa ɗaya tilo da ta maida martani mai tsananin ƙarfi ga gwamnatin Sahyoniya ita ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Gwamantin da idan ta mamaye wani wuri, ba za ta ja da baya ba kuma ba zata yarda da tsagaita wuta ba; sai dai idan an tilasta mata yin hakan, tabbas babu shakka, ƙarfin soja, tsaro, da kimiyya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi mummunan lahani ga wannan gwamnatin a cikin yakin kwanaki 12, ta yadda wannan gwamnatin ta nemi tsagaita wuta; kuma wannan yana nuna iko da karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Da yake magana game da wayewar Iran mai zurfi, wadda ba ta taɓa karɓar a mulketa ba, Birgediya Janar Nasirzadeh ya ƙara da cewa: Amurka tana da girman kai a zahiri kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da ra'ayin 'yancin kai. Waɗannan halaye biyu suna cikin rikici da juna. Mika wuya bai taɓa dacewa da asalin Jamhuriyar Musulunci da tarihin Iran, da kuma al'ummar Iran ba.
A yau, muna cikin yanayi inda dole ne a binciki kowane batu kuma a gamsu da shi. Dole ne ɗalibi ya ga ko cikakken hoton da wasu mutane ke zanawa ya yi daidai da gaskiya ko a'a.
Bai kamata ɗalibi ya yi magana a cikin son rai ba. Ya kamata ɗalibi ya yi karatu, ya ga fannoni daban-daban na batutuwan, sannan ya yi hukunci.
Your Comment