Hizbullah Ta Mayar Da Martanin Ga Gargaɗin Amurka Ga Lebanon

Isra'ila: Yaƙi Da Hizbullah A Lebanon Ba Makawa Ne
28 Oktoba 2025 - 13:50
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Mayar Da Martanin Ga Gargaɗin Amurka Ga Lebanon

Wakilin Amurka na musamman Tom Barak ya gargaɗi manyan jami'an Lebanon guda uku cewa dole ne su fara tattaunawa kai tsaye da Isra'ila; in ba haka ba, za su fuskanci rikici wanda ba a san ƙarshensa ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya jaddada a martanin da ya mayar wa masu shiga tsakani na ƙasashen duniya cewa Hizbullah a shirye take ta kare makamanta kuma wannan matsayin ba wai kawai wani shiri na soja ba ne.

Kafafen watsa labarai na Ibrananci sun tabbatar da cewa: Yaƙi Da Hizbullah A Lebanon Ba Makawa Ne

Domin suna cewa: Isra'ila ta sanar da Amurka cewa Hizbullah ta shigo da ɗaruruwan makamai masu linzami daga Siriya

Gabaɗaya, wasu daga cikin kalaman Isra'ila suna fakewa da su ne kawai saboda ayi yaƙi, duk da sake ginawa da Kera makamai na Hizbullah suna gudana cikin sauri. Saboda hakane Isra'ila ta ga abin da Hizbullah ta ke yin a cewa ba ta durkushe ba, kuma yanzu tana gyara wurarenta, shi ya sa Isra'ila ke son dakatar da ita da wuri-wuri.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha