28 Oktoba 2025 - 09:56
Source: ABNA24
Jirgin Saman Ɗaukar Kaya Na Sojojin Amurka Ya Sauka A Siriya

Jirgin saman ɗaukar kaya na sojojin Amurka ya sauka a arewacin Hasakah domin ƙarfafa kasancewar sojojin haɗin gwiwa a gabashin Siriya

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Majiyoyin yankin sun sanar da cewa wani jirgin saman ɗaukar kaya na sojojin Amurka, tare da helikwafta na yaƙi, ya sauka a sansanin Kharabul-Jir da ke arewacin lardin Haskah domin ƙarfafa kasancewar sojojin haɗin gwiwa na ƙasashen duniya a arewa maso gabashin Siriya.

Jirgin da aka ambata a sama yana ɗauke da kayan lantarki, manyan makamai da wasu jami'an soja kuma ya shiga yankin tare da ba da kariyar wani jirgin helikwafta na yaƙi.

A cewar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Siriya, waɗannan yunkuri suna faruwa ne a ci gaba da aikin ƙarfafa matsayin ƙungiyar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa a arewa maso gabashin Siriya.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Siriya ta ƙara da cewa: A jiya, a matsayin wani ɓangare na kasancewarsu a yankin, dakarun haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa sun aika da sabbin ƙarin sojoji zuwa arewa maso gabashin Siriya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha