21 Oktoba 2025 - 13:25
Source: ABNA24
Al-Jubouri: Amurka Ta Tanadi 'Yan Kungiyar ISIS 11,000 A Syria Domin Kai Hari Iraki

Wani dan Majalisar Wakilan kasar Iraki ya bayyana cewa: Amurka ta ajiye 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish su 11,000 a kasar Siriya domin su yi amfani da su a kan Iraki a nan gaba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Thaer Al-Jubouri dan majalisar dokokin kasar Iraki ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai cike da cece-ku-ce daga tsarin hadin gwiwa: Amurka ta ajiye 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish su 11,000 a kasar Siriya domin amfani da su wajen yaki da Iraki a nan gaba.

A wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Al-Ma’aluma, Al-Jubouri ya ce: “Amurka ba ta son kafa kwarya-kwaryar runduna masu fafutuka a Iraki, kuma ta yi kokari ta hanyoyi daban-daban wajen kawo cikas ga dokar Hashdush Sha’abi, saboda wannan runduna ta iya yin tsayin daka gaba da gaba wajen fuskantar ta’addanci.

Ya kara da cewa: Amurka da kawayenta na yahudawan sahyoniya sun ajiye 'yan kungiyar ISIS 11,000 daga cikin dakarun da suke da alaka da su a kasar Siriya; wadannan mutane sun taru daga kasashe daban-daban na duniya domin goyon bayan Amurka da gwamnatin sahyoniyawan.

Al-Juboi ya kuma yi iƙirarin cewa "Amurkan, ta hanyar wadannan ‘yan kungiyar isis a Siriya, suna burin lalata Iraki da keta hurmin wanna kasa’ ta hanyar raunanar da Hashdush Sha’abi suna kokarin zartar da shirunsu ne a kan Iraq".

Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da Washington ta sha nanata cewa kasancewar sojojinta a Siriya na da nufin yakar ragowar mayakan ISIS da kuma tallafawa zaman lafiyar yankin. To sai dai kuma, wasu rigingimun siyasa a Iraki sun nuna shakku game da hakikanin manufofin Amurka a yankin.

.................................

Ƙarshen saƙo / 7976

Your Comment

You are replying to: .
captcha