21 Oktoba 2025 - 08:42
Source: ABNA24
Jagora: Samuwar Amurka A Yankin Gabas Ta Tsakiya Shike Haifar Da Yake-Yake

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake ishara da irin shirmen da shugaban kasar Amurka ya yi a baya-bayan nan dangane da yankin da kuma kasar Iran, ya ce: Shugaban kasar Amurka ta hanyar zuwa Palastinu da aka mamaye da kuma fadin wasu tarin maganganun shirme tare da nuna rashin gaskiya ya yi kokarin sanyawa sahyoniyawan da suka yanke kauna fata,

Jagoran ya yi la'akari da irin mari mai ban mamaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi wa gwamnatin sahyoniyawan a yakin kwanaki 12 a matsayin dalilin yanke kauna inda ya kara da cewa: Sahayoniyawan ba su yi tsammanin cewa makamin Iran zai iya kutsawa cikin zurfin cibiyoyinsu masu muhimmanci da harshen wutarsu ​​da kuma lalata wadannan cibiyoyi da mayar da su toka ba.

Yayin da yake jaddada cewa Iran ba ta saya ko hayar makaman daga ko'ina ba, sai dai wadannan makamai kirar hannu ne da kuma katin shaida na matasan Iran, Ayatullah Khamenei ya ce: A lokacin da matasan Iran suka shiga fagen da kuma samar da ababen more rayuwa na ilimi da kokari suna iya cimma irin wadannan abubuwa masu girma.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Dakarun mu da masana'antun soji sun riga sun shirya wadannan makamai masu linzami, sun yi amfani da su, kuma har yanzu suna da su, kuma idan ya cancanta za su yi amfani da su a wani lokacin.

Bayan da ya takaita dalilin wannan shirmen na Trump na kalamai masu laushi da dabi'ar kwarkwasa don kara kwarin gwiwar yahudawan sahyoniyawa, ya ci gaba da bayyana wasu 'yan abubuwa game da da'awowin Trump inda ya ce: A yakin Gaza, babu shakka Amurka ita ce babbar abokiyar tarayya a laifuffukan gwamnatin sahyoniyawan, kamar yadda shugaban Amurka da kansa ya amince cewa muna aiki da wannan gwamnati a Gaza. Tabbas in da bai fadi haka ba ma to da ta fito fili domin kayan aiki da makaman da aka zuba wa mutanen Gaza marasa tsaro a lokacin wannan yakin na Amurka ne.

Ayatullah Khamenei ya kira sauran da'awar Trump na cewa Amurka na yaki da ta'addanci wani misali na karyarsa ya kuma kara da cewa: Sama da yara da jarirai 20,000 ne suka yi shahada a yakin Gaza. Su 'yan ta'adda ne? Amurka ce ’Yar ta’adda, wacce ta kirkiro ISIS take ruguza yankin, kuma a yau wasu sun tabbatar da shi a wani yanki sun ajiye shi don amfanin kansu.

Haka nan kuma ya bayyana kisan da aka yi wa kimanin mutane 70,000 a yakin Gaza da kuma shahadar Iraniyawa fiye da dubu a yakin kwanaki 12 a fili karara kan irin ta'addancin Amurka da gwamnatin yahudawan sahyoniya, ya kuma bayyana cewa: Baya ga kisan mutane baji ba gani, sun kashe masana kimiyyar mu irinsu Tehranchi da Abbasi tare da yin alfahari da wannan laifi, amma su sani ba za su iya kashe ilimi ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kalaman shugaban na Amurka, wanda a yayin da yake alfahari da kai harin bama-bamai kan masana'antar nukiliyar Iran da kuma ikirarin ruguza ta, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: "Babu wata matsala, kai ta rudar kanka akan hakan, amma to kai meye ruwanka idan har wata kasa tana da masana'antar nukiliya?, da har zaka ce wannan ya kamata ko wannan  bai kamata, shin me ye ruwan Amurka don Iran tana da makaman nukiliya da masana'antu ko ba ata da shi?, wannan tsoma ba ki da katsalandan hauragiya ne.

Yayin da yake ishara da zanga-zangar adawa da Trump a fadin kasar baki daya da mutane miliyan 7 suka yi a jahohi da garuruwa daban-daban na Amurka, ya ce: Idan kana da karfin gaske, maimakon yada karya da kai kutsa cikin al'amuran wasu kasashe da daukar matakai kamar gina sansanonin soji a cikinsu, ka kwantar da hankulan wadannan miliyoyin mutane, ka mayar da su gidajensu.

Ayatullah Khamenei ya kuma jaddada cewa Amurka it ace ta'addanci da hakikaninsa, Ayatullah Khamenei ya kuma bayyana ikirarin Trump na goyon bayan al'ummar Iran a matsayin karya, ya kuma kara da cewa: Takunkumin da Amurka ta kakabawa al'ummar Iran a karo na biyu, wanda kasashe da dama kuma suke goyon bayansa saboda tsoro, yana kan al'ummar Iran ne, don haka kai makiyin al'ummar Iran ne ba masoyinsu ba.

Yayin da yake ishara da furucin da Trump ya yi na shirye-shiryen kulla yarjejeniya, ya ce: Ya ce shi mai son kulla yarjejeniya ne, amma yayin da idan yarjejeniyar ta kasance tare da tilastawa kuma an san sakamakonta tun da farko, to ba yarjejeniya ba ce, kawai tazamo tirsasawa da tilastawa. Al'ummar Iran ba za su mika wuya ga tilastawa ba.

Yayin da yake ishara da sauran kalaman Trump dangane da wanzuwar mutuwa da yaki a yankin yammacin Asiya, ko kuma kamar yadda suke kira, Gabas ta Tsakiya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ishara da cewa: Ku kuka fara kagar yake-yake. Amurka ce mai kirkirar yaki ce kuma baya ga ta'addanci, tana kuma tunzura yaki. In ba haka ba, menene manufar duk wadannan sansanonin sojojin Amurka a yankin? Me kuke yi a nan? Menene alakar wannan yanki da ku? Yankin dai na al'ummar yankin ne, kuma yakin da ake yi a wannan yanki, samuwar Amurka ne ya haddasa shi.

A karshe Ayatullah Khamenei ya yi ishara da cewa batutuwan shugaban kasar Amurka kuskure kuma a lokuta da dama karya ce kawai kuma tana nuni da cika baki, sannan ya jaddada cewa: Duk da cewa cika baki yana da tasiri a kan wasu kasashe, amma da yardar Allah ba zai taba yin tasiri a kan al'ummar Iran ba.

A wajen wannan biki, tawagar tsoffin matasan kasar sun gudanar da wani yunkuri na wannan wasa, wadanda suka samu yabo da girmamawa daga Jagoran juyin juya halin Musulunci.

Your Comment

You are replying to: .
captcha