Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma janyewar sojojin yahudawan sahyuniya, kasuwannin yankin Al-Jalaa da ke cikin birnin Gaza sun dawo da cigaba da ayyukansu, inda suka shaida yadda mutane ke kaiwa da komowa. ‘Yan kasar Falasdinu, wadanda aka hana su shiga kasuwanni na tsawon lokaci saboda hare-haren sojin Isra’ila, yanzu sun koma saye da sayarwa da samar da muhimman kayayyaki don biyan bukatunsu na yau da kullun tare da bude wadannan cibiyoyin kasuwanci.

21 Oktoba 2025 - 11:42
Source: ABNA24

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha