Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta sanar da cewa, kasashen Afghanistan da Pakistan sun cimma matsaya kan dakatar da fadace-fadace da kuma tsagaita bude wuta a wani zagayen tattaunawa da aka gudanar a birnin Doha na kasar.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, kasashen biyu sun kuma amince da gudanar da tarukan bi da bi domin tabbatar da dorewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta bayyana fatan cewa, wannan mataki zai taimaka wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a kan iyakokin kasashen biyu da ke makwabtaka da su, da kuma zama ginshiki mai daurewar zaman lafiya a yankin.
Tun da farko ma'aikatar tsaron gwamnatin Taliban ta sanar da cewa, Maulvi Mohammad Yaqub Mujahid, ministan tsaron gwamnatin kasar ya isa birnin Doha bisa jagorancin wata tawaga da za ta tattauna batun kan iyaka da bangaren Pakistan.
A bangare daya, ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta sanar da cewa, wata tawagar Pakistan karkashin jagorancin ministan tsaron kasar ta isa birnin Doha domin tattaunawa da bangaren Afghanistan. Sanarwar ta ce: Pakistan ba ta neman tada jijiyar wuya, sai dai tana son bangaren Afganistan ya kiyaye hakkinsa na kasa da kasa da kuma magance matsalolin tsaron Pakistan da kuma daukar mataki kan kungiyoyin 'yan ta'adda na Khyber, da Taliban na Pakistan, da kuma kungiyoyin 'yantar da Balochistan.
Tuhumar Juna Tsakanin Kasashen Biyu
A cikin 'yan kwanakin nan, zargin da ake yi wa juna tsakanin Afganistan da Pakistan kan rikicin kan iyaka ya karu. "Mohammad Nabi Omari," mataimakin ministan harkokin cikin gida na gwamnatin Taliban, ya zargi sojojin Pakistan da suka kai hare-hare ta sama a lardin Paktika da ke gabashin Afganistan a ranar Juma'a, da cewa ba su yi wannnan harin ba ne da kashin kansu ba, sun yi ne bisa aiwatar da umarnin shugaban Amurka Donald Trump.
Ya ce: "Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan wata dama ce ta kwato yankunan da aka kwace daga Afghanistan." Ya kara da cewa, bisa tilas ne aka sanya layin Durand tsakanin Afghanistan da Pakistan.
Jami'in na Afganistan ya kuma jaddada cewa, kungiyar Taliban ta Pakistan, wadda Islamabad ke zargi da kai hare-haren ta'addanci, ba a kasar Afganistan aka kafa ta ba, kuma ba a kafa ta a lokacin gwamnatin Taliban ba, kuma ba ta da goyon bayan gwamnatin Taliban.
Sabanin haka, babban hafsan sojin Pakistan Asim Munir a ranar Asabar din da ta gabata ya zargi Indiya da ci gaba da manufofin ta na ta'addanci da kuma amfani da 'yan ta'adda da ke Afganistan a matsayin sojojin haya a kan Pakistan. Ya ce an dauki wadannan matakan ne bayan fatattakar hare-haren da Indiya ta kai wa Pakistan.
Da yake magana a wajen bikin yaye gungun jami'an sojin Pakistan, ya ce: "Dole ne tsarin Afghanistan ya dakatar da dakarunsa daga yin amfani da kasar Afganistan a matsayin mafaka wanda daga can suke kai munanan hare-hare kan Pakistan".
Your Comment