Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Majiyoyin yada labarai na Isra'ila sun rawaito cewa sojoji 3 na sojojin mamaya sun jikkata sakamakon fashewar wani bam a yammacin gabar kogin Jordan.
Kafofin yada labarai na Ibraniyawa sun dauki wannan lamarin a matsayin wani abu mai hatsarin gaske na ci gaba da kai hare-hare kan sojojin yahudawan sahyoniya.
Your Comment