18 Oktoba 2025 - 19:59
Source: ABNA24
Maariv: Kashi 13 Cikin 100 Ne Kawai Na Isra'ilawa Suka Ɗauki Yakin Gaza A Matsayin "Cikakken Nasara"

Sakamakon wani bincike da jaridar Maariv ta Isra'ila ta gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa, al'ummar Isra'ila sun samu sabani wajen tantance sakamakon yakin baya-bayan nan a Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: sakamakon wani bincike da jaridar Maariv ta kasar Isra’ila ta gudanar a baya-bayan nan, ya nuna cewa al’ummar Isra’ila sun samu sabanin ra’ayi kan sakamakon yakin baya-bayan nan a Gaza.

Bisa ga binciken, kashi 46 cikin 100 na masu amsa sun yi la'akari da cewa Isra'ila ta samu "nasara ta musamman," yayin da kashi 13 ne kawai ke kiranta hakan da "cikakkiyar nasara." Kashi 35 cikin 100 kuma sun yi imanin cewa Isra'ila ba ta cimma nasara ba kwata-kwata.

Wasu 'yan jaridun Isra'ila kuma sun soki sakamakon yakin. Ronen Bergman na Yedioth Ahronoth ya nuna shakku kan abin da ke cikin yarjejeniyar sirrin da Isra'ila ta rattabawa hannu a Sharm el-Sheikh, yayin da Avi Issacharoff ya ce babu wata nasara saboda Hamas ta ci gaba da rike Gaza. Ben Caspit ya kara da cewa, a halin yanzu kungiyar Hamas ce ke iko da kashi 85 cikin 100 na yankunan Gaza, kuma tana daukar matakan murkushe wadanda ake zargi da hada kai da Isra'ila.

Binciken da sharhin da aka yi na nuna shakku da rashin gamsuwa a tsakanin al'ummar Isra'ila game da sakamakon yakin Gaza, wanda ake ganin yayi nesa da abin da ake tsammani.

Your Comment

You are replying to: .
captcha