Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Ali al-Miqdad, babban jami'I mai goyon bayan kungiyar gwagwarmaya a majalisar dokokin kasar Lebanon a daren jiya a jawabin da ya gabatar game da abubuwan da suke faruwa a kasar, musamman ci gaba da fadada hare-haren wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawa, ya ce gwamnatin kasar ba ta cika aikinta na dakatar da hare-haren Isra'ila da fara sake gina kasar ba.
Ali al-Miqdad ya bayyana a yayin wani taron siyasa da ofishin hulda da jama'a na kungiyar Hizbullah ya gudanar a birnin Dhalil a cikin kwarin Bekaa: "Mun bar batun dakatar da wuce gona da iri na makiya da batun sake gina kasar ga gwamnati da ta dauki mataki, amma abin bakin ciki shi ne kusan shekara guda ke nan da tsagaita bude wuta, kuma gwamnatin Labanon ba ta dauki matakin diflomasiyya da na siyasa ba, ya kamata a ce gwamnatin kasar ta Lebanon ta dauki matakin dakatar da hare-haren ta'addanci a kasar Lebanon. Wanda a yankin da a yanzu suka mamaye kaso 7 maimakon 5, kuma a sako fursunonin Lebanon, tare da fara aikin sake gina kasar".
Your Comment