12 Oktoba 2025 - 09:55
Source: ABNA24
Gwamnatin Jamus Ta Na Yarjejeniya Da Taliban Kandawo Da 'Yan Gudun Hijirar Afghanistan

Gwamnatin Jamus ta sanar da cewa tana gab da cimma yarjejeniya da Taliban don gudanar da jigilar jigilar 'yan gudun hijirar Afganistan akai-akai.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Gwamnatin Jamus ta sanar da cewa tana dab da kulla yarjejeniya da kungiyar Taliban na gudanar da jigilar komawar 'yan gudun hijirar Afganistan akai-akai; wani mataki da ke gudana bisa tsarin tsauraran manufofin shige da fice na Jamus.

Ministan cikin gidan Jamus Alexander Dobrindt ya ce "Tattaunawar ta ci gaba sosai, don haka za mu iya tunanin za mu cimma matsaya nan ba da jimawa ba".

A wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta The Pioneer, ya bayyana cewa Berlin na da niyyar gudanar da ayyukan kora a kai a kai, kuma hakan ba wai yana nufin amfani da jiragen haya ne kadai ba, har da jiragen kasuwanci.

Shi ma shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Mertz, wanda ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, ya kuma yi alkawarin hanzarta korar 'yan gudun hijirar Afganistan da aka samu da laifi a Jamus.

Wannan yunkuri mai cike da cece-kuce na zuwa ne bayan Jamus ba ta amince da gwamnatin Taliban ba bayan da ta koma kan karagar mulki a watan Agustan 2021. Tun daga wannan lokacin ne Berlin ta gudanar da ayyukan korar 'yan kasar Afganistan sau biyu kacal.

Your Comment

You are replying to: .
captcha