1 Satumba 2025 - 15:34
Tarihin Irin Tsananin Tsaro Da Abbasiyawa Su Kai Kan Imam Hasanul Askary As 

Tarihin Irin Tsananin Tsaro Da Abbasiyawa Su Sanya Kan Imam Hasanul Askary As Don Kar A Haifi Imam Mahdi As.

Ahmad dan Ubaidullah dan Khaqan ya siffanta Imam As da cewa:

Khulainy ya ruwaito daga Husain dan Muhammadul Ash’ary da Muhammad dan Yahaya da wasun su’ sunce:” Ahmad dan Ubaidullah dan Khaqan ya kasance shi ke kula da wurare da dukiyar haraji na Qum’ wata rana a majalissar sa ya faru an anbaci batun Ulawiyyawa da mazhabarsu’ ya kasance mai tsattsauran Ra’ayi dangane da su’ sai yace: ban ga ko sanin wani mutum Ba’ulawiyye a garin Sirri man Ra’a irin Hasan dan Ali dan Muhammad dan Ridhaa wajen kyautar sa da nutsuwar sa da kame kansa da kaifin hankalin sa’ da karamcin sa cikin Iyalan gidan Manzon Allah da Bani Hashim’ hakanan a wajen jagorori da wazirai dama sauran mutane’ domin wata rana ina tsaye bisa kusa da mahaifina wanda rannan shine yake gudanar da majlisi ga mutane’ sai masu ison sa suka shigo su kace: Abu Muhammad dan Ridah yana a bakin kofa’ sai yace da sauri da karfi: ku yi masa izini’ sai nayin mamakin abun da naji daga wajen sa domin naji yadda suke bakan tashi wajen Babana kuma ba kowa a wajen ban da Khalifah ko kuma magajinsa’ ko wanda sarki ya masa kinaya da hakan’ sai ga wani mutum ja mai kyakkyawan zubi’ mai kyakkyawan fuska mai kyan jiki mai kananan shekaru yana cikin daukaka da kwarjini yayin da baba yayi duba zuwa gareshi sai ya tashi yana tafiya zuwa gareshi da kafafunsa, kuma ban san ya taba yin irin wannan ba ga wani daga Banil Abbas da jagorori ba, yayin da ya kusanta gareshi sai ya rungume shi tare da sunbatar fuskar sa da kirjinsa‘ sannan ya kama hannunsa ya zaunar dashi kan abun sallarsa da ya kasance yana zaune akai’ sannan ya zauna akusa dashi yana mai fuskantarsa da fuskarsa’ sannan ya fara Magana dashi yana mai dadin bakin kan zamowa fansa agareshi sai nayin mamakin abun da nagani daga gareshi; sai kawai dan Ison shi ya ce: Muwaffaq yazo, kuma ya kasance idan Muwaffaq zai shigo wajen Babansa akwai masu ja masa gaba musamman jagororinsa sai suka tashi atsaye agaban majalasinsa da tsakanin kofar Samadin har ya zuwa shigowarsa da fitarsa’ amma bai gushe ba yana fuskantar Abi Muhammad yana mai yi masa Magana har sai da yayi dubi zuwa ga kebantatttun masu yi masa Hidima’ sai yace alokacin: idan kaso – Allah yasanya ni na zamo fansarka- sannan yace ga masu yi masa Iso: ku dauke shi zuwa bayan Kofar Samadiin don kar wannan ya ganshi - yana nufin Muwaffaq ne – sai ya tashi shima babana ya tashi ya rungume shi sannan ya tafi.

Sai nace da masu yiwa Babana iso da bayinsa kenan: tir daku waye wannan da kuka shigar da shi wajen Babana’ kuma Babana yayi masa irin wannan aiki?

Sai suka ce: wannan Ba’alawiyye ne ana ce dashi Alhasanu dan Ali an sanshi da sunan Ibnur Ridha sai na kara yin mamakinsa ban gushe ba a wannan ranar ina cikin damuwa da tunani dangane da lamarin sa da lamarin Babana da abunda nagani dangane da haka, har dare yayi’ ya kasance ya saba yin sallar Atmah (sallar Ishai ) sannan ya dan zauna ya duba abubuwan da yake da bukatarsu na shirye-shirye da abubuwan da zai gabatar da su ga Sarki yayin da ya gma sallar ya zauna sai na zo na zauna a gabansa ba wani atare dashi sai yace dani: Ya kai Ahmad kana da wata bukata ne?.

Sai nace: Na’am Ya Babana’ waye mutumin da na ganka da safe kayi masa abunda kayi masa na daukakawa da karamci da girmamawa ka fanshe shi da kanka da mahaifanka?.

Sai ya ce yakai dana: wancanenka shine shugaban Rafidawa shi ne Hasan dan Ali’ wanda akafi sani da Ibnur Ridha’ sai yayi shiru na dan lokaci’ sannan yace: ya kai Dana da ace khalifanci ya gushe daga Khalifofin Banil Abbas to da ba wanda zai cancance shi daga Bani Hashim koma bayan wannan’ lalle wannan ya cancanci khalifanci saboda falalarsa da kamun kansa da shiriyarsa da kiyayewarshi da gudun duniyarsa da ibadarsa da kyawawan halayensa da ingancinsa. Da ace kaga Babansa da kaga cikakken madaukakin mutum’ mai kaifin hankali kuma madaukaki.

Sai na kara damuwa da shiga tunani da kunci sosai akan Babana da abunda naji daga gareshi kuma damuwar ta karu sosai ganin abunda ya fada tare da aikatawa ga shi’’ bayan wannan bani da wani aiki banda tanbayar labarin sa da binciken lamarinsa’ ban taba tanbayar wani daga Bani Hashim da Jagorori da marubuta da Alkalai da Malaman Fiqihu da sauran mutane sai na samu yana mai girmama shi da daukaka da matsayi madaukakinsa’ da daddaden zance da kuma gabatar da shi sama ga dukkan iyalan Gidan sa da malumansa, sai matsayinsa ya girmama a wajena don banga masoyi ko makiyi sa mun same shi yana kyautata zance tare da yabo gareshi ba.

Sai wasu daga cikin wadansu Ash’arawa da suka halarci majalisin sa suka ce: ya kai Ababakar to ya labarin dan uwan sa Ja’afar?.

Sai yace: waye kuma ja’afar da za kama tanbayi labarinsa’ ko harma a gwama shi da Hasan? Ja’afar din da yake bayyana fasikanci fajiri mara kunya’ mashayin giya’ irinsa daga cikin mutane yan kadan nagani wanda ya fisu tozarta kan shi acikinsu’ rago mai kaskanta kansa’ hakika ya shiga wajen Sarki da yan fadarsa alokacin da Hasan dan Ali yayi wafati sai nai mamakinsa ban tsammanin haka yake ba, wannan ya faru ne yayin da Imam Hasan yayi rashin lafiya’ ya aika zuwa ga Babana cewa: Lalle Ibnur Ridha yana rashin lafiya’ sai ya hau abun hawa alokacin ya nufi fadar Khalifanci’ sai ya dawo cikin gaggawa a tare dashi akwai masu yiwa Khalifa hidima guda biyar dukkansu sun kasance daga kebantattun kuma amintattunsa’ daga cikin akwai Nahrir’ ya umarce su dasu lazimci gidan Hasan don su samu labarin yanayinsa’ ya kuma tura wasu daga cikin Mutadalliben (ƴan leken asiri)ya umarcesu da su lazimce shi su dunga bibiyarsa safe da rana. Bayan hakan ya kasance da kwana biyu ko uku sai labari yazo cewa jikin sa yayi rauni sosai’ sai ya umarci Mutadalliben da lazimtar gidansa’ ya kuma aika akira masa Alkali yazo ya sameshi wajen majalasinsa ya umarci daya zabi mutane goma daga mutanensa da ya yarda dasu wajen addininsu da amanarsu da tsoron Allansu’ ya zo da su sai ya aika su zuwa gidan Hasan’ ya umarce su da su lazimci shi dare da rana basu gushe ba acen har sai da yayi wafati As’ garin Sirriman Ra’a ya girgiza ya cika da kuka’ sarki sai ya aika zuwa gidan sa wasu domin su bincika dakunan gidan su kuma rubuta tare da qididdige duk abunda ke cikin gidansa’ su kai binciken inda Dan sa yake suka zo da mataye da suke gane mata masu ciki suka shiga wajen kuyangin sa suna dudduba su’ sai wasunsu suka fadi cewa akwai wata baiwa mai juna biyu sai suka san yata acikin wani daki suka wakilta hadimi Nahrir da mutanensa da wasu mata domin su kula da ita.

Sannan bayan haka suka fara shirya shi aka kuma bada hutu na kasauwanni’ sanna Banu Hashim da Jagorori da mahaifina da sauran mutane suka hau dawakansu domin rakiyar janaizarsa’ SirriMan Raa a ranar ta zamo kamar ranar Kiyama’ bayan sun gama shiryashi sai sarkin ya aika zuwa ga Abi Isa dan Mutawakkil yana mai umartarsa da yayi masa salla’ yayin da aka ajiye gawarsa domin yi mata salla sai Abu Isa ya kusanto gareshi ya yaye fuskar sa ya nunawa Bani Hashim na bangaren Alawiyyawa da Abbasawa da Jagorori da marubuta da Alkalai da masu Matsakaitan matsayi sannan yace: wannan shine Hasan dan Ali dan Muhammad dan Ridha ya mutu kawai hakan dakanshi akan wannan shinfidarsa’ kuma ya samu halartar hadiman Amiril Mu’uminin da amintattatunsa: wane da wane daga Alkalai: wane da wane’ daga Mutadallibeen: wane da wane sannan ya rufe fuskarsa ya umarta da a daukeshi daga tsakiyar gidan sa a bunneshi a gidan da aka bunne mahaifinsa.

Yayin da aka bunne shi sai sarkin da mutane suka fara binciken Dan sa’ kuma ya yawaita bincike acikin wurare da gidaje’ suka saurara wajen raba gadon sa’ wadanda aka wakilta domin kula da baiwar nan da suke mata tsammanin tana da ciki suna masu lura da ita har saida rashin cikin ya bayyana’ yanayin ciki ya baci garesu sai aka raba gadonsa tsakanin mahaifiyarsa da dan uwansa Ja’afar.

Sai mahaifiyar ta riya cewa yayi wasiyya kuma an tabbatar da ita wajen Alkali. Ga kuma Sarkin yana ta binciken inda Dan sa yake.

Shi kuwa sarkin bai gushe ba yana mai neman inda Dan Hasan dan Ali yake .

Mun kawo wannan Nassin da tsayin sa saboda abunda yake dauke dashi na fa’idodi masu yawa za muyi nuni zuwa ga su anan kasa:

Na farko – bayanin matsayin Imam As harma ga wadanda ba yan shi’arsa da masoyansa ba’ kuma cewa shi wannan matsayin da soyayyar na cikin zukatan ta kasance lamari ne na Ubangiji.

Na Biyu – cewa Matsayin Imamanci matsayi ne na Allah ba ya karbar saukewa ko dagawa daga fuskacin Mutane ko ya matsayin su yake, kuma maganar Ubaidaullah dan Khaqan da yayi ga Ja’afar ishara ce zuwa ga hakan- yayin da ya tambaye shi akan ya nada shi a matsayin dan uwansa Imamul Askary As-: ya kai wawa sarki fa ya zare takobinsa ga wadanda suka riya…..”.

Na Uku – Nassin yana haska mana cewa yanayin yadda sarki yake mu’amala da Imam As alokacin rashin lafiyarsa da yayi wafati, da kuma shaidar da ya bayar na cewa wafatinsa ya kasance na dabi’a ne. hakan ya tunantar damu mu’amalar Harunar Rashid ga Imam Musa dan Ja’afar As, kuma yana tabbatar da kasancewar Imam yayi wafati ne ta hanyar bashi guba, kuma yana kara tabbatar da hakan: ko kari na tsarewa tare da yunkurin kisa wanda akai nuni da shi a baya, da kuma kasancewar ya rasu yana saurayi ne, da kuma cewa rashin lafiyarsa ta fara farkon wata sannan yayi wafati a takwas ga gashi .

Na Hudu- tsananin tsoro na Sarki ga samuwar dan Imam As, wanda ya nuna wajen bincike gidajensa da wurare da kuma taskace duk abunda ya mallaka, da kuma sanya tsaro mai tsanani ga kuyanginsa, tare da tsare wadanda yake tsammanin suna da ciki, dukkan wadannan abubuwa suna nuni da tsananin tsoron da sarki ya sanya na ya zamo Imam As yana da Da, kamar tsoron Fir’auna dangane haihuwar Annabi Musa As, wannan kuwa lamari da ba’a saba dashi ba na wani daga cikin masu mulki na zamaninsu yayi irin wannan mu’amala din ga daya daga cikin A’immah a baya ba.

Abun da yake qarara shine dalilin da ya kaisu ga haka shine irin labaran da ya iso maso dangane da sha’anin Imamul Mahdy As kuma cewa za’a haifeshi daga Imamul Hasan As idan ba haka ba to ba bukatar duk wannan tsanantawa; domin ana haifarsa ya kasance karkashin kulawa da tsarewa ta dole kamar sauran A’immah As.

Your Comment

You are replying to: .
captcha