Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya kawo rahotan cewa: an gudanar da zaman makoki na ranar shahadar Imam Jafar Sadik (AS) tare da jawabin HUjjatul Islam "Sayyid HUssain Momini" da waken jaje daga Sayyid Ali HUssaininajad a cikin hubbaren Imam Khumaini (RA) Shabestan na Haramin Sayyidah Ma'asumah (As).
Al'ummar Musulmai mabiya mazhabar Shi'a a faɗin duniya sun gudanar da zaman makokin shahadar Imam Sadik (a) shugaban mazhabar shia Imamiya a daren jiya da yau.