Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya habarta cewa: Wasu ‘yan bindiga sun kai wani mummunan hari a jihar Zamfara ta Najeriya, inda suka yi garkuwa da mutane sama da 100. Jami’an yankin da kuma dattawan kasar sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane biyu tare da yin garkuwa da mutane sama da 100 yawancinsu mata da kananan yara, a wani mummunan hari da suka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A cikin ‘yan watannin nan jihar Zamfara ta Najeriya ta zama cibiyar hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda aka fi sani da ‘yan bindiga. Wadannan hare-haren sun sanya tafiye-tafiye da ayyukan noma a yankin cikin matukar hadari. Rahoton na SBM ya nuna cewa, an yi garkuwa da mutane 4,722 a jihar Zamfara ta Najeriya tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.
Shugaban kauyen Mohammed Mai Anjua ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa maharan sun isa ne a kan babura da dama a yankin Adabka Bukkuyum da ke kauyen Gandum Malam inda suka bude wuta.
Wani mazaunin kauyen Huzaifa Issa ya bayyana cewa maharan sun kasu kashi biyu ne: bangare daya da aka tura domin yin garkuwa da mutane da dabbobi, yayin da daya kuma suka kafa shingen bincike a babbar kofar shiga kauyen inda suka bude wuta kan mutanen da ke kokarin wucewa.
Your Comment