23 Agusta 2025 - 17:05
Source: ABNA24
Imam Rida (AS) Daٍ Salon Manufofin Gwagwarmaya

Gwagwarmayar Imam bai takaitu ga fagen siyasa kadai ba, a'a ta kai ga bangaren al'adu da ilimi. Domin a cikin wa'azi da muhawara da tattaunawa a cikin al'umma Imam ya kasance yana tunatar da mutane akidar Imamanci na hakika.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya kawo cewa: siyasar Imam Ali bn Musa al-Rida (a.s) tana cike da tsattsani da dabara wajen tunkarar shuwagabanni azzalumai; arangama da ta hada riko da ka’idoji da hikima da wayo.

A zamanin Al-Ma'amun al-Abbas, a lokacin da halifanci ke fama da rikicin halalcinta a shari’ance, Al-Ma'amun ya yi yunkurin yin amfani da matsayin Imam Rida (a.s) na ruhi da zamantakewa don tabbatar da mulkinsa. Sai dai Imam ya fuskanci wannan makirci da wata manufa da za a iya kiranta da ita "Gwagwarmaya ta Hankali", yana mai dakile shirin Al-Ma'amun mataki-mataki.

Babban abin da ya fi fitowa daga wannan gwagwarmayar shi ne batun gadon sarauta. Ta hanyar nada Imam a matsayin yarima mai jiran gado, Al-Ma'mun ya nemi halascin ikon gwamnatinsa. Sai dai Imam Rida (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yarda da hakan bisa tilastawa da barazanar kisa, kuma ya gindaya sharuddan da suka baca makircin Ma'amun daga kowane irin abu. Mafi muhimmanci daga cikin wadannan sharudda shi ne cewa ba zai tsoma baki cikin harkokin siyasa ko na gwamnati ba, yana mai isar da sako karara cewa: karbuwarsa a hukumance ba yana nufin amincewa da halaccin gwamnatin Abbasiyawa ba.

Gwagwarmayar Imam bata takaitu ga fagen siyasa ba; ta kai ga fannin al'adu da tunani. Domin a cikin wa'azin khudubobin da muhawarori da tattaunawa a cikin al'umma Imam ya kasance yana tunatar da mutane akidar Imamanci na hakika.

Hadisin “Sarkar Zinare” da ya fada a cikin birnin Nishapur babban misali ne na hakan, inda Imam ya jaddada cewa Tauhidi ba ya cika sai da riko da waliyyar Imamin gaskiya, a fakaice bayyana rashin halascin mulkin Ma’amun. Don haka Imam ya yi amfani da kayan aikin al'adu da tunani wajen ruguza tushen halalcin mulkin Abbasiyawa.

Haka nan Imam Rida (amincin Allah ya tabbata a gare shi) bai taba bari a ce an san shi da hukuma ba. A yanayi kamar Sallar Idi, ya nuna salo mai zaman kansa wanda ke bayyana darajarsa tare da fallasa karyar aikin al-Ma'amun. Hakan ya san Maa’amun ya kara rudewa, har sai da ya rasa mafita face ya kawar da Imam ta hanyar sanya masa guba.

Sake karanta wannan siyasar a yau tana koyar da mu darussa masu mahimmanci: Gwagwarmaya a gaban ma'abota girman kan ba yana nufin ja da baya ko kuma gazawa ba, a'a yana nufin kiyaye iyakokin akida da siyasa da amfani da duk wata dama ta al'adu da hankali don fallasa karya da makircin mahukunta. Imam Rida (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya tabbatar da cewa gwagwarmaya agaban zalunci ba ya bukatar takobi; Hakanan ana iya samun ta ta hanyar kalmomi, matsayi, da kuma sani. Don haka, Rayuwarsa ta siyasa ta kasance abin koyi maras shudewa ga kowane zamani da lokaci wajen fuskantar zalunci da mulkin kama karya.

Muhammed Haeri Shirazi

Your Comment

You are replying to: .
captcha