19 Agusta 2025 - 22:35
Source: ABNA24
Sheikh Zakzaky: Shirin Yahudawan Sahyoniya Na Korar Mutanen Gaza D Makaman Hizbullah Ba Zai Cimma Nasara Ba

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa shirin da gwamnatin ke yi na mayar da Falasdinawa zuwa kudancin Gaza tare da tsugunar da su a tantuna ci gaba ne na tsawon shekaru biyu na kisan kare dangi ta hanyar yunwa da tashin bamabamai. Ya jaddada cewa ainihin dalilin da ke tattare da wadannan ayyuka shi ne yadda ake amfani da albarkatun kasa na Gaza ta hanyar da bai dace ba, musamman ma'adinan iskar gas.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A wata tattaunawa ta musamman da shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Yaqoub Zakzaky H ya yi da kafar yada labaran kasar Iran, ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin sahyoniyawan ta dauka a baya-bayan nan, yana mai bayyana cewa yunkurin da take yi na korar Falasdinawa daga Gaza da kuma kwance damarar mayakan Hizbullah ta hanyar matsin lamba ga gwamnatin Labanon abu ne mai wuyar gaske.

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa shirin da gwamnatin ke yi na mayar da Falasdinawa zuwa kudancin Gaza tare da tsugunar da su a tantuna a matsayin ci gaba ne na tsawon shekaru biyu na kisan kare dangi ta hanyar yunwa da tashin bamabamai. Ya jaddada cewa ainihin dalilin da ke tattare da wadannan ayyuka shi ne yadda ake amfani da albarkatun kasa na Gaza, musamman ma'adinan iskar gas.

"Hukumar yahudawan sahyoniya na shirin shafe al'ummar Gaza ba su damu ba ko hakan na nufin kashe kowa da kowa, bayan shafe shekaru biyu ana gudanar da kisan kiyashi ta hanyar amfani da bama-bamai da yunwa, a yanzu suna son ta hanyar korar tilas, su sace albarkatun Gaza, musamman ma iskar gas, amma hakan zai cimma nasara ba. Falasdinawa ba za su bar kasarsu ba, daga kogi zuwa teku," in ji shi.

Da ya koma Magana kan kasar Labanon, Shaikh Zakzaky ya soki irin matsin lambar da ake yi wa kungiyar Hizbullah na ta mika makamanta, yana mai bayyana hakan a matsayin wata dabara ta kokarin raunana karfin gwagwarmayar. Ya jaddada cewa, karfin kungiyar Hizbullah ba ya ta'allaka ne a cikin makamanta ba, sai dai yana ta’allaka ne a cikin imaninta da goyon bayan jama'a.

Ya kara da cewa "'Yan sahyoniya suna tunanin kwance damarar Hizbullah zai raunana su, amma hakikanin karfinsu shi ne imani da Allah. Lebanon ba za ta zama wata gabar yammacin kogin Jordan ba, al'ummar kasar suna tsaye tare da Hizbullah a matsayin masu kare su."

Kalaman nasa sun yi daidai da na babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem, wanda a baya-bayan nan ya yi gargadin cewa kwance damarar gwagwarmayar zai kasance tamkar mika tsaron Lebanon ga Isra'ila.

Jawaban Shaikh Zakzaky suna kara jaddada falsafar tsayin daka da gwagwarmaya da ke kafe a kan imani na ruhi da kuma bijirewa hare-haren hadin gwiwa na Isra'ila da Amurka.

Your Comment

You are replying to: .
captcha