Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: Sheikh "Naim Qassem" babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya yi jawabi a wajen taron tunawa da shahadar babban kwamandan jihadi Sayyid Fouad Shukr (Sayyid Mohsen) a yankunan kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon.
A farkon taron, ya ce: Muna aiki akan tafarki guda biyu; Tafarkin gwagwarmaya don 'yantar da ƙasa daga Isra'ila, tafarki na biyu, tafrkin yin ayyukan siyasa don gina ƙasa. Ba ma fifita ko wane tafarki, kuma ba ma maye gurbin ɗaya akan ɗayan ba, amma muna tafiya a kan tafarkin biyu a lokaci guda. Saboda haka, babu yiwuwar tattaunawa tsakanin waɗannan hanyoyi guda biyu.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ci gaba da cewa: Zaben Joseph Aoun a matsayin shugaban kasa ya zo ne bayan shafe shekaru ana fama da rikici da gajiyar tsarin mulki. Gwagwarmaya ta hanyar sauƙaƙe wannan tsari, ta sake nuna cewa tana ɗaya daga cikin manyan ginshiƙai na ginin hukumar. Tambaya sassauka a nan: Ta yaya za a gina hukuma a kasar Lebanon? Wasu ba su san mene ne manufarsu ta gina kasa ba: shin sun zo ne domin su yi sata ko don su kawar da wani bangare na al’umma?
Sheikh Naim Qassem, yayin da yake ishara da samuwar gwagwarmayar ya bayyana cewa: Wannan gwagwarmaya ta fito ne a matsayin mayar da martani ga mamaya, tare da cike gibin da sojojin Lebanon suke da shi, kuma sun samu 'yantacciyar 'yanci a shekara ta 2000. Wannan gwagwarmaya tana ci gaba kuma tana da alhakin dakile Isra'ila da kare Lebanon. Wannan gwagwarmaya ba ta taɓa ɗaukar wani matsayi ko alhakin kowa ba. Jami’an tsaro ne ke da alhaki za su kasance masu daukar nauyi. Al'umma ita ce mai alhakin hakan kuma za ta dauki nauyi. Muna alfahari da wannan hadin kai kuma muna cewa wannan gwagwarmaya tana da nauyi daya ga sojoji da kuma jama'a. Ba wai kawai muna rera taken ba ne, sai dai mun yi imani da wannan hakikar kuma mun yi imanin cewa duk yadda wadannan bangarorin uku suka kara yin karfi da hadin kai, za a samu mafi kyawun nasarorin.
Ya yi ishara da yarjejeniyar bayan yakin Ulil –Ba’as ya ce: Mun fuskanci zaluncin Isra'ila kuma an cimma yarjejeniya wadda na tabbbar da cewa Isra'ila ce ta nema. Ga Isra'ila, ya zamo Hizbullah ta janye daga kudancin kogin Litani da maye gurbinsu da sojojin Lebanon, wata nasara ce. A namu ra’ayin gwamnati ta dauki nauyin kare kasar nan nasara ce. Wannan yarjejeniya ta sami fa'ida a gare mu da abokan gaba. Mun taimaka wa gwamnati, amma Isra’ila ba ta bi yarjejeniyar ba. Wannan yarjejeniya ta shafi kudancin Litani ne kawai. Idan wani yana ganin akwai alaka tsakanin yarjejeniyar da makamai, to ya kamata ya san cewa makamai batu ne na cikin gida na kasar Labanon kuma ba shi da wata alaka da Isra'ila.
Sheikh Naim Qassem ya jaddada cewa: Bayan yakin Al-Bas na farko, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare, amma ba da karfin gaske ba, kuma da nufin matsawa kungiyar Hizbullah da Lebanon ta yada cewa Hizbullah ta yi rauni saboda ba ta mayar da martani ba. Muka ce lokacin da gwamnati ta karbi alhakin, ba mu da aikin mayar da martani mu kadai. Wannan yana nufin cewa dukkanin dakarun siyasa suna da alhakin. Sun yi tsammanin Hizbullah ta yi rauni, amma sun yi mamakin ganin kasancewar Hizbullah a cikin tsarin gwamnati, a kudancin kasar, da kuma gagarumin gudanar da jana'izar shahidai irin su Sayyid Hassan Nasrallah da Sayyid Hashem Safiyyuddin. Sun kuma yi mamakin sakamakon zaben. Duk wannan yana nuna cewa gwagwarmaya tana da ƙarfi a cikin kowane fanni na siyasa, zamantakewa, lafiya, da ayyuka. Ya kara da cewa: Isra'ila ta karya yarjejeniyar kuma tana ci gaba da yin barazana. Mun dauki wannan a matsayin sakamakon hadin gwiwa tsakanin Isra'ila da Amurka. Amurka, tare da lamunin Hochstein, ta yi alkawarin bin diddigin yadda Isra'ila ta aiwatar da yarjejeniyar, amma sai ta aike da wakili wanda burinsa shi ne haifar da rikici a Lebanon. Maimakon taimakawa, Amurka tana lalata kasarmu don taimakawa Isra'ila.
Sheikh Naim Qassem ya ce: Barak ya zo da barazana da tsoratarwa cewa zai shigar da kasar Labanon cikin kasar Sham kuma za a cire ta daga taswirar kasar, amma ya kadu matuka da irin matsayin da 'yan Lebanon suka dauka a hade, da kasa da kuma gwagwarmaya. Ya yi tunanin cewa zai haifar da fitina ta hanyar matsa wa shugabannin uku, amma bai san cewa suna sane da irin abubuwan da ke faruwa a Labanon ba. Amurka na son mayar da Lebanon wani makami na sabon aikin gabas ta tsakiya da kuma lalata karfinta.
Ya ci gaba da cewa: An tabbatar da tsaro a arewacin yankunan da aka mamaye tsawon watanni takwas, amma har yanzu ba a ikata hakan a kasar Labanon ba. Har yanzu Isra'ila na ci gaba da zama a wuraren kan iyaka biyar don samun makaman Hezbollah karkashin tallafin Amurka. Manufarsu ita ce hana Lebanon ikon soja daga baya, ta hanyar raya wadannan yankuna, gina matsuguni da tsoma baki a harkokin siyasar cikin gida. Wannan shi ne abin da ya faru a Siriya.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana halin da ake ciki a kasar Labanon cewa: Muna fuskantar wata barazana ta wanzuwa, ba wai kawai ga gwagwarmaya ba, har ma ga daukacin kasar Lebanon, da dukkanin kabilunta da al'ummarta. Hadarin ya fito ne daga Isra'ila, ISIS da Amurka. Ba wai kawai suna son ɗaukar makaman gwagwarmaya ba ne, sai dai suna son mamaye ƙasar Lebanon. Me yasa suke hana mutane komawa kauyukan kan Iyaka?
Ya ce cikin kakkausar murya: Ba za mu sayar wa Isra’ila Lebanon ba. Na rantse da Allah, idan duk duniya ta hade kai a kanmu, ko da an kashe mu duka, Isra’ila ba za ta taba cin galaba a kan mu ba, ko kuma ta kwace Lebanon. Makaman mu na gwagwarmaya ne da Isra'ila kuma ba ruwansu da harkokin cikin gidan Lebanon. Wannan makamin shine ikon Lebanon. Duk wanda ke son mika makaman yana son gabatar da su ne ga Isra'ila.
Ya ce: Mu mutane ne masu girma da daraja, mun yi imani da koyarwar Imam Husaini (AS) da ya ce: “ba zamu dauki kaskanci ba”. Za mu ba da kariya ko da ya kai ga shahada. Ba za mu zama karkashin mamaya ba. Muna nan daram saboda muna da gaskiya.
Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: Dole ne gwamnatin Lebanon ta cika ayyukan da suka hau kanta; Dakatar da ketara iyaka da sake gina wurin da aka lalata. Idan Amurka na hana taimakon kasashen waje, dole ne gwamnati ta samar da wasu hanyoyin magance su. Har ila yau, sake ginawa yana da amfani ga tattalin arzikin kasar.
Dangane da shahidi Sayyid Fouad Shukr babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa: Sayyid Mohsen ya kasance daga Beka'a kuma daya daga cikin kwamandojin soji na Hizbullah na farko. Shi ne shugaban ƙungiyar da aka sani da alkawarin maza goma; dukkansu sun yi shahada. Ya yi mubaya'a ga Imam Khumaini sannan kuma ga Imam Khamene'i. Ya halarci manyan ayyuka a kudancin Lebanon, Bosnia, da kuma a yakin 2006. Ya kasance mai kula da rundunonin sojan ruwa na shahada na Hizbullah, kuma yana daya daga cikin wadanda suka tsara wannan shahararriyar farmakin da aka kai. Ya kuma taka rawar gani a yakin Dufanul Aqsa. Mutum ne mai imani, jajircewa, tawali’u, da tunani mai kirkira. Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalansa da dukkan masoyansa na rashinsa.
Daga karshe ya yi ishara da shahadar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyah ya kuma kara da cewa: Wannan shahada ita ce ci gaba da tafarkin gwagwarmayar Palastinu, wanda ke kan gaba a duniya a yau, muna shaida yadda ake kashe kananan yara da mata a Gaza ta fuskar laifukan Amurka da sahyoniya, kuma kungiyoyin kasa da kasa suna ba da bayani ne kawai. Dole ne a ba da garantin dakatar da wadannan laifukan ta’addancin. Ya yaba wa fursunan mai gwagwarmaya, George Abdullah, ya kuma yi ishara da cewa: "Shi misali ne na gwagwarmaya wanda ya ci gaba da zama a gidan yari tare da girmamawa tsawon shekaru 41. gwagwarmaya ta dukkan mutane ne da kabilu ce, kuma dukkanmu mun hade kan 'yantar da Falasdinu.
Your Comment