Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa: Dakarun kasar Yemen sun sanar da cewa sun kai wani samame na musamman ta hanyar harba makami mai linzami a birnin "Beer-Saba" da ke kudancin Isra'ila.
Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yaman ya kuma sanar da cewa, kungiyar ta kai hari kan muhimman wurare a garuruwan "Eilat", "Ashkelon" da "Al-Khudeira" da jirage marasa matuka guda uku.
Ya yi gargadin cewa, ana la'akari da wasu hanyoyin da za a iya kara kai hare-hare, kuma ana daukar wadannan matakan ne a matsayin martani ga ci gaba da ta'addanci, da yaki da yunwa da kisan kare dangi a Gaza.
A gefe guda kuma Sojojin kasar Isra’ila sun sanar da dakile wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen. A halin da ake ciki kuma, na'urorin gargadi na sojojin Isra'ila sun yi ta kararrawa a yankunan gabar yamma da kogin Jordan, da hamadar Negev da kuma kewayen Tekun Mutuwa.
A baya dai sojojin na Isra'ila sun ce sun gano wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yaman kuma suna kokarin kakkaboshi. A lokaci guda kuma, an buga hotuna a shafukan sada zumunta da ke nuna karar fashewar wasu abubuwa da suka ce karar hare-haren na’urar tsaron Isra'ila ne suka haddasa.
Wadannan hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kasar Yemen suka kara kai hare-haren makami mai linzami da jiragen sama a kan yankunan Isra'ila da suka hada da filin jirgin sama na Ben-Gurion da tashar jiragen ruwa na Eilat a cikin 'yan makonnin nan.
...................................
Your Comment