Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: Riyad Mansour, wakilin din-din-din na kasar Falasdinu a MDD, a yayin zaman da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a daren ranar Laraba, kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, a lokacin da yake ba da labarin mummunan bala'in da likitan Falasdinawan Alaa al-Najjar ta shiga, wacce ta rasa 'ya'yanta tara a asibitin Nasser bayan da sojojin Isra'ila suka yi ruwan bama-bamai a gidansu, inda ya yi magana ta hanyar yin kukan bakin ciki dabuga damatsansa kan batun.
Ya ce cikin wata murya mai daci: Hotunan yadda iyaye mata ke rungumar gawar 'ya'yansu marasa rai, suna wasa da gashin kansu, suna magana da ba su hakuri... Wannan abu ne da ba za a iya jurewa ba.
Dangane da iyalansa, Mansour ya kara da cewa: Ina da jikoki kuma na san muhimmancinsu ga iyalansu. Ganin halin da Falasdinawa suke ciki ba tare da daukar mataki ba ya fi karfin dan Adam.
Wakilin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya ya kammala da kalaman bacin rai: "Wuta da yunwa suna cinye 'ya'yan Falasdinu, shi ya sa mu Falasdinawa muke fushi a ko'ina".
Masu amfani da kafofin watsa labarun, ciki har da Platform X (tsohon Twitter), sun bayyana yanayin a matsayin mai mutuƙar kuncin dan Adama da raɗaɗi. Wani mai amfani ya rubuta: "Kukan jakadan Mansour ya kasance mafi sahihanci martani ga bala'in Gaza. Ba taken gwagwarmaya ko cin zarafin siyasa na jinin mutane ba kamar wadannan hawaye".
Riyad Mansour ya kuma yi kakkausar suka ga kalaman Benjamin Netanyahu, wanda ya musanta cewa akwai yunwa a Gaza. Mansour ya ce: "A kan wace hujja ya fadi haka? Isra'ila ta kama dubban Falasdinawa, ta nuna su rabin tsirara a gaban kyamarori tare da ikirarin cewa ba sa yunwa?"
Wannan jawabi ya yadu a kafafen yada labarai da ra'ayin jama'a a duniya.
Your Comment