Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya nakalto maku cewa: A wani jawabi mai cike da basira da kaifin ƙwaƙwalwa, da ya gabatar wa almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) a garin Hadeja, Sheikh Yaqoub Yahaya Katsina ya bayyana cewa har yanzu, duk da ƙalubale da jarrabawa, 'yan uwa suna ci gaba da kasancewa a tsaye, masu riƙo da jagorancin da aka gada daga Sayyid (H). Ya ce: "Hatta waƙi'ar 2015 bata iya raba 'yan uwa da jagorancin ba".
Sheikh Yaqoub ya ƙara jaddada cewa, ‘yan uwa a cikin Harka na da manyan hadafi guda biyu: Na farko, mutum ya samu tsira a gaban Allah (SWT) ta hanyar sauke nauyin da aka ɗaura masa. Na biyu kuma, shi ne samun ƙiyadar jagoranci ba tare da rarrabuwa ba koda kuwa an samu bambance-bambancen fahimta ko ra’ayi.
"Babban abu mai wahala, Allah ya sauƙaƙa mana. Na farko shi ne yin Bara'a da Zalunci da Kafurci. Abu na biyu kuma shi ne ƙiyadar jagoranci," in ji Malamin, yana mai jaddada cewa waɗannan abubuwa biyu su ne ginin Harka.
Ya bayyana cewa, duk da irin fitinar da ta afku a shekarar 2015 wadda ta girgiza al’umma, da rarrabuwar kai da aka jefa almajiran Sayyid (H) a ciki, hakan bai karya jagorancin ba. A cewarsa, "Ko da an ce Malam ba ya cikinmu, 'yan uwa suna tsaye akan jagorancinsa. Wannan babbar ni’ima ce da Allah ya ba mu".
Sheikh Yaqoub ya bayyana cewa, makasudin maƙiya shi ne su fasa ginin jagoranci ta hanyar haifar da rarrabuwar kai. Amma hakan bai yi tasiri ba a wajen almajiran da suka san darajar jagora da manufa. "Sun gama daku idan har suka rabaku da jagorancinku," in ji shi, yana mai nuna yadda wannan salon ya hallaka gwagwarmayar wasu ƙasashe da dama.
Ya ƙara da cewa, bambancin fahimta da ganewa ɗabi’a ce ta ɗan Adam, kuma ba matsala ba ce matuƙar jagoranci yana nan da ƙa’ida da matsin lamba, yana mai ƙarfafa gwiwar su ci gaba da kasancewa cikin tsari da biyayya.
Jawabin ya gudana ne a ranar Alhamis, 2 ga Nuwamba, 2023, a ya yin wata ganawa ta musamman da 'yan uwa a Hadeja.
Wanda Rubuta: Hassan Ɗan Sister Katsina
Litinin 26/05/2025M.
Your Comment