7 Janairu 2021 - 12:10
Iran: Dakarun BASIJ Sun Fara Gudanar Da Atisaye A Cikin Tekun Fasha

Dakarun sa kai na Basij na kasar Iran sun fara gudanar da wani gagarumin atisayi a cikin tekun fasha, da jiragen ruwa na yaki guda 700.

ABNA24 : Rahotanni sun ce dakarun na Basij sun fara gudaar da wannan atisayi nea yau Alhamis daga gabar ruwan kasar Iran ta Bandar Abbas, inda suke sintiri da gwada makamai a cikin jiragen ruwa na yaki guda 700.

Wannan atisayin dai yana zuwa nea daidai lokacin da zaman dar-dar ke karuwa a yankin, sakamakon barazanar da makiyan kasar ta Iran suke yi a kanta.

A cikin wanann makon da ya gabata ne Amurka ta aike da babban jirgin ruwa da ke dauke da jiragen yaki zuwa cikin tekun fasha, wanda kuma hakan na zuwa ne a lokacin da wasu bayanai na sirri ke ishara da cewa, mai yiwuwa Donald Trump ya gigin kaddamar da hari kan Iran kafin ya bar mulkin Amurka.

A nasa bangaren babban kwamandan dakarun IRGC na Iran Janar Hussain Salami ya bayyana cewa, sun kammala dukkanin shirinsu domin tunkarar kowace irin barazana daga makiya.

342/