ABNA24 : Da akwai mutane da dama da suka gabatar da kawunansu domin ayi gwajin allurar rigakafin da su
Kwamitin da yake aiwatar da umarnin Imam Khumaini ( R.A.) ne ya samar da rigakafin, kuma gwajin na farko an yi shi ne akan diyar shugaban kwamitin. Wasu daga cikin wadanda aka yi wa allurar rikagafin a yau sun hada da shugabannin kwamitin.
Tun bayan bullar cutar ta corona, Iran ta bude bincike akan hanyoyin samar da rigakafinta, da kuma daukar tsauraran matakai na dakile ta.
A cikin makwannin bayan nan, ana samun koma bayan yaduwar cutar a Iran, haka nan kuma wadanda suke rasa rayukansu saboda ita.
342/