ABNA24 : A cikin watannin bayan nan dai an sami ci gaba na azo a gani ta fuskar zaman lafiya da sulhu a tsakanin bangarorin da suke fada da juna a kasar ta Libya.
Kasashen Moroko da Tunisiya sun taka rawa wajen karbar bakuncin zaman tattaunawa a tsakanin banagrorin gwamnatocin Libya da suke da matsugunai da Tripoli da kuma Tubruk.
Kasashen larabawa sun rabu gida biyu a tsakanin masu goyon bayan janar Halifa Hfatar da yake iko da gabashin kasar, da kuma gwamnatin al-Siraj mai matsuguni a Tripoli.’
342/