13 Disamba 2020 - 10:47
Gwamantin Jihar Katsina Ta Sanar Da Rufe Dukkan Makarantun Kwana A Fadin Jihar

A wata sanarwa da gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari ya fitar ya bada umarnin rufe dukkan makarantun kwana a fadin jihar baki daya, biyo bayan harin da ‘yan bindiga dake garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa suka kai a wata makarantar kwana ta Sakandiren gwamnati dake garin kankara.

ABNA24 : Harin da ‘yan bindiga suka ka kai tun a daren Juma’ar da ta gabata ya jawo bacewar yara da dama daga makarantar baya da wasu dalibai da dama da suka tarwatse suka watsu a cikin daji saboda firgici.

Ya zuwa yanzu dai ba’a tantance adadin yawan daliban da suka bace ko aka sace ba sakamakon afkuwar wannnan lamari.

A nasa bangaren shugaban Nigeria Mohammadu buhari ya umarci da a aike da karin dakarun tsaro zuwa inda abin ya faru domin gano da kwato dukkan daliban da ‘yan bindingan suka Sace.

Matsalar tsaro dai na ci gaba da yin kamari a fadin Nigeria musamman a Arewacin kasar duk da kokarin da mahukumta suka ce su na yi na kawo karshen matsalar.

342/