ABNA24 : Dakarun kare juyin musulunci na Iran ne su ka kamo Zam, bayan da ya dauki lokaci yana yana amfani da kafar telegram wajen watsa labarun karya akan Iran da kuma yi wa kungiyoyin leken asirin waje aiki.
Ruhullah Zam ya kasance a kasar Faransa inda daga can yake aiwatar da ayyukansa na batunci ga juyin musulunci, sai dai dakarun kare juyi sun yi nasarar dawo da shi gida inda ya fuskanci shari’a.
342/