ABNA24 : Muahhamd Yazdi ya rike mukamin alkalin alkalan Iran ne daga tsakanin 1988 zuwa 2008, sannan kuma ya zama memba a majalisar kwararru mai zamabar jagoran juyin musulunci.
Wasu daga cikin makaman da ya rike da akwai babban sakataren majalisar koli ta cibiyar ilimi ta Hauza da kuma sakataren majalisar shawarar musulunci ta Iran sau biyu.
Har ila yau marigayin ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai
“Ususul-Iman Fil Qur’an.
Nabzah Min Ma’ariful-Islamiyyah.
Ya rasu ne dai a yau Laraba yana dan shekaru 89.
342/