ABNA24 : Sa’idzadeh ya kara da cewa; Wasu kasashen sun zubar da duk wani mutunci da suke da shi, domin su cimma manufofinsu a zamanin shugaban Amurka mai barin gado.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Wadannan kasashen sun kuma kashe makudan kudade domin su sami yardarm shugaban Amurka da ya fadi a zabe.
Har ila yau, ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta bakin kakakinta ta dorawa Saudiyya alhakin mawuyacin halin da Yemen take ciki na yunwa da yaki da zubar da jini.
342/