28 Nuwamba 2020 - 12:39
Kasar Venezuela Dawo Ta Da Cinikin Danyen Man Fetur Da Sin Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Amurka Da Turai

Gwamnatin kasar Venezuela ta sake dawo da cinikin danyen man fetur da kasar Sin duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dora mata.Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa kamfanin man fetur na kasar ta Venezuela ya dawo da cinikin danyen man fetur da kamfanin man fetur na kasar Sin CNPC.

ABNA24 : Labarin ya kara da cewa an dakatar da cinikin danyen man fetur ko makamashi da kasar ta Sin ne, a cikin watan Augusta na shekara ta 2019 a lokacinda kasashen Amurka da Turai suka shelanta takunkuman tattalin arziki mai tsanani ka kasar ta Venezuela.

Amma bayan tallafin da ta samu daga kasar Iran a cikin ‘yan watannin da suka gabata, a halin yanzu kasar Venezuela ta sai da ganga miliyon 1.8 na danyen man fetur ga kasar ta Sin.

Kasashen Amurka ta Turai dai suna zargin shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro da magudi a zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a shekara ta 2019 wanda kuma ya lashe.

Banda haka, Amurka ta na da wani dan adawar kasar ta Venezuela Joe Guado a matsayin halattaccen shugaban kasar Venezuela a wajenta.(19)

342/