28 Nuwamba 2020 - 12:37
Siriya: Mutane 4 Ne Suka Mutu Ko Suka Ji Rauni Sanadiyyar Tashin Nakiya A Arewacin Kasar Siriya

Wata nakiya wacce ‘yan ta’adda suka bari a lokacinda suke mamaye da arewacin kasar Siriya ta tashi ta kuma fashe, inda ta yi sanadiyyar mutuwar yara biyu da kuma raunata wasu biyu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Siriya SANA ya bayyana cewa a jiya da dare ne wata nakiya wacce aka bisne a kasa a garin Abushoora na Lardin Rikka a arewacin kasar Siriya ta tashi sannan ta yi sanadiyyar kashewa da raunata yara 4.

Labarin ya kara da cewa a lokacinda yan ta’adda suka kwace iko da wasu yankuna a arewacin kasar ta Syriya sun binne nakiyoyi, da boma-bomai a wurare da dama, daga cikin har da gidajen mutane da abubuwan wasan yara, wadanda a halin yanzu suka zama matsala ta tsaro da zaman lafiya ga mazauna wadannan wurare.

Labarin ya kammala da cewa tashe-tashen nakiyoyi ko boma–bomai irin wannan zai ci gaba da cutar da mutanen kasar Siriya na shekaru aro-aro masu zuwa. (19)

342/