23 Nuwamba 2020 - 17:44
​Zarif: Iran Da Syria Za Su Ci Gaba Da Yin Aiki Tare Domin Ci Gaban Al’ummominsu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya jaddada cewa, kasashen Iran da Syria za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin fagage, domin ci gaban al’ummominsu.

ABNA24 : Zarif ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa ta wayar tarho tare da sabon ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Miqdad, wanda a jiya shugaba Bashar Assad ya nada a shi a matsayin ministan harkokin wajen Syria, bayan rasuwar tsohon ministan harkokin wajen kasar Walid Mu’allim a ranar Lahadin da ta gabata.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad Zarif, ya taya Faisal Miqdad murnar samun wannan matsayi, inda ya yi masa fatan alhairi, da kuma yi ma al’ummar kasarsa hidima, kamar yadda kuma ya kara mika sakon ta’aziyya dangane da rasuwar walid Mu’allim.

Zarif ya ce alaka tsakanin Iran da Syria alaka ce ta tarihi, wadda ba za ta girgizu ba sakamakon matsin lamba, kamar yadda kuma har kullum kasar ta Iran za ta ci gaba da kasacewa tare da Syria cikin kowane irin yanayi.

Shi ma a nasa bangaren sabon ministan harkokin wajen kasar ta Syria Faisal Miqdad ya yi jinjina dangane da irin kyakkyawar alaka da ke tsakanin kasashen biyu, tare da bayyana cewa Iran da Syria kasashe ne masu kawance mai karfi na ‘yan uwantaka.

342/