22 Nuwamba 2020 - 13:31
​Rauhani Ya Taya Al’ummar Lebanon Murnar Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin kai

Shugaba Hassan Rauhani na kasar Iran ya aike wa takwaransa na kasar Lebanon da sakon taya murnar zagayowar ranar da kasar ta Lebanon ta samu ‘yancin kai.

ABNA24 : A cikin sakon nasa shugaba Rauhani ya bayyana cewa, yana taya takwaransa shugaba Micheil Aoun da sauran dukkanin al’ummar kasar Lebanon zagayowar ranar da kasar ta samu ‘yancin kai daga turawa ‘yan mulkin mallaka.

Ya ce a cikin shekarar da ta gabata kasar Lebanon ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa, amma sakamakon hikimar jagororin al’ummar kasar, a karkashin shugabancin Aoun, kasar ba ta fada cikin mawuyacin hali kamar yadda wasu suke fata ba.

Shugaba Rauhani ya ci gaba da cewa, gwagwarmaya irin ta al’ummar kasar Lebanon wajen neman hakkokinsu da rayuwa a cikin ‘yanci na siyas ada zamantakewa da tsaro, shi ne babban sirrin duk wata nasara da suka samu tun daga lokacin mulkin mallaka, har zuwa yanzu.

Daga karshe ya yi fatan alhari da samun ci gaba mai albarka da zaman lafiya ga kasar, da ma dukkanin al’ummomin yankin da na duniya baki daya.

342/