ABNA24 : Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya bayar da shawarar a sauyawa jami’ar nazarin ci gaba wacce a takaice ake kira da ( UDS) zuwa sunan Jerry John Rawling wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki kadan da su ka gabata.
Shugaban kasar ta Ghana y ace, Jerry Rawlings ne shi kadai ya zage damtse ya yi tukuru na kafa wannan jami’ar a lokacin rayuwarsa, duk da matsalolin da ya fuskanta.
Shugaba Akufo Addo ya kara da cewa; Marigayi Jerry Rawlings ba mutum ne wanda yake son a rika sanya sunayensa a kan wasu cibiyoyi ba, amma dai duk da haka ya cancanci a girmama shi.
342/