14 Nuwamba 2020 - 11:14
Rundunar Da Take Fada Da “Yan Taádda A Yankin Sahel Ta Sanar Da Kashe Kwamandan Kungiyar Alqaída

Rundunar sojan ta hadaka wacce kasar Faransa take jagoranta da ake kira da “Barkhane” ce ta sanar da kashe Bah Agh Moussa a kasar Mali wanda kuma MDD ta shigar a cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.

ABNA24 : A jiya Jumaá ne dai rundunar ta yankin Sahel ta sanar da cewa ta kashe Agh Moussa ne a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kasar Faransa tana da dubban sojoji a cikin yankin Afirka ta yamma da suke aiki tare da sojojin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka, wajen fada da ‎masu ikirarin jihadi.

Da akwai kungiyoyi da dama masu ikirarin jihadi a cikin yankin na sahel da su ka hada da al’qaida.

Kasashen da suke fama da matsalolin tsaro a yankin sun kunshi Mali, Niger, Burkina Faso, Cameroon da Chadi.

342/