13 Nuwamba 2020 - 14:30
Bangarorin Da Ke Rikici A Libiya Sun Cimma Yarjejeniyar Gudanar Da Zabe A Kasar

Bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar Libiya sun amince da shirin da aka gabatar a yayin tattaunawar da MDD take jagoranta na gudanar da zabubbuka a kasar cikin watanni 18 masu zuwa da nufin kawo rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar.

ABNA24 : Wakiliyar MDD ta wucin gadi kan kasar Libiyan Stephanie Williams ce ta shaida wa manema labarai bayan bangarorin sun cimma matsaya a taron sulhu da suke gudanarwa a kasar Tunusiya inda ta ce wakilan bangarorin sun cimma matsaya kan wata yarjejeniyar aiki da nufin kawo karshen gwamnatin rikon kwarya da kuma tsara ingantaccen zabe na shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Wakiliyar MDD ta kara jaddada wajibcin yin dukkanin abin da za a iya wajen ganin an gudanar da tsaftataccen zabe da kuma samar da abubuwan da al’ummomin kasar suke bukata wajen gudanar da rayuwarsu cikin sauki da kwanciyar hankali.

A kwanakin baya ne dai aka fara gudanar da wannan taro na tattaunawa a kasar Tunusiya da nufin samar da hanyar da za a kawo karshen yakin da ke gudana a kasar Libiya ta hanyar samar da wata gwamnati ta wucin gadi wacce za ta shirya zabubbuka a kasar da nufin kawo karshen yakin da ke ci gaba da faruwa a kasar.

A halin yanzu dai kasar Libiyan tana karkashin ikon kungiyoyi masu dauke da makami da kuma gwamnatoci biyu: gwamnatin Tripoli wacce kasashen duniya suka amince da ita da kuma majalisar da ke iko da gabashin kasar da ke samun goyon bayan kwamandan sojojin gabashin Janar Khalifa Haftar.

342/