ABNA24 : Mahaifin Rawlings dan kasar Scotland ne a yayinsa mahaifiyarsa ‘yar kasar Ghana. Rowlings ya kammala makarantar sojojin sama a shekara 1969 a birnin Accra. Sannan ya jagoranci juyin mulki har sau biyu a kasar, wato a shekara ta 1979 da kuma 1981.
Sai kuma daga karshe Rawlings ya mika shugabancin kasar ta Ghana ga John Kufour wani dan jam’iyyar adawa a kasar a shekara ta 2001.
Daga nan ne ya zama uban kasa, inda yake shiga tsakani don kyautata lamuran kasar a duk lokacinda ake bukatan hakan. Rawlings har’ila yau ya taba zama jakadan kungiyar Tarayyar Afirka Au a kasar Somalia.(19)
342/