ABNA24 : Shugaba Rouhani ya bayyana haka ne a taron kasashen kungiyar wanda aka gudanar a safiyar yau Talata ta kafafen sadarwa na hotunan bidiyo, wanda kuma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya jagoranta.
Rouhani ya kara da cewa akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen yakar cutar korona a kasashen kungiyar, sannan kasar Iran a shirye take ta bayar da nata gudumawar, da kuma irin ci gaban da ta samu a yakar wannan cutar.
A fagen tattalin arziki kuma, shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, za’a kammala shimfida layin dogo daga birnin Rasht zuwa tashar jiragen ruwa ta Injali na bakin tekun Caspian, wanda zai hada arewa da kuma kudancin kasar Iran da layin dogo.
Daga karshe shugaban ya bayyana farin cikinsa da kawo karshen yaki tsakanin kasashen Azarbejan da Armeniya. Ya kuma yabawa gwamnatin kasar Rasha da kokarin da ta yi na tabbatar da zaman lafiya a kasashen biyu, wadanda suka kasance makobtaka da kasar Iran.
342/