ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Sarki Muhammad na 6 yana fadin haka bayan tashe-tashen hankula da suka fara a garin Al-Kalkarat na kan iyakar kasar da kasar Mauritayi a cikin ‘yan makonnin da suka gabata.
Sarkin ya kara da cewa gwamnatin kasar tana kan shawarar MDD dangane da warware rikicin kudancin kasar.
Tun shekara ta 1975 ne gwamnatin kasar Morocco ta mamaye yankin yammacin Sahara, bayan da dakarun turawan Espaniwa yan mulkin mallaka suka fice daga kasar.
Kungiyar Polisario dai ta mutanen yankin yammacin sahara ne wadanda suke gwagwarmayan samun ‘yenci daga kasar Morocco tun lokacin, tare da daukar makamai.
342/