ABNA24 : Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Alkalan kotun sun yi watsi da kalubalantar sakamakon zaben da shugaban yan adawa Cellou Dalein Diallo ya gabatar, bayan ya samu kashi 33 da rabi, sabanin kashi 59 da rabi da shugaba Conde ya samu.
Diallo ya shaida wa kotun cewa; alkaluman da wakilansa suka tattara a tashoshin zabe sun nuna masa cewar shi ya samu nasara.
Yayin da wakilan kungiyar kasashen Afirka da na ECOWAS suka amince da sahihancin zaben, kasar Faransa da kungiyar kasashen Turai da kuma Amurka sun bayyana shakku game da sakamakon.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun mamaye gidansa kafin gabatar da matsayin kotun, yayin da 'yan Sandan kwantar da tarzoma suka tare hanyar zuwa gidansa domin hana shi ganawa da manema labarai.
Da wannan hukunci na kotu, yanzu shugaba Conde mai shekaru 82 ya kama hanyar yin sabon wa’adi da kuma damar sake yin takara idan ya kammala wannan wa’adin, sakamakon sauya kundin tsarin mulkin kasar da ya yi.
342/