ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Spotnik na kasar Rasha ya nakalto hukumar kula da filayen Falasdinawa karkashin kungiyar PLO ta na fadar haka.
Ta kuma kara da cewa wannan adadinin rushe-rushe shi ne mafi muni a tarihin gwamnatin yahudawan .
Labarin ya kara da cewa a shekara ta 2016 ma gwamnatin yahudawan ta rusa gidajen Falasdinawa 123.
Har’ila yau Labarin ya kara da cewa rushe-rushen gidajin Falasdinawa na wannan shekarar ya auku ne mafi yawa a birnin Qudus.
Kuma sun auku ne bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya shelenta “Yarjejeniyar Karni” a cikin watan Jenerun wannan shekara (19).
342/