‘Yan kallo na kungiyar Tarayya Turai da na wasu kasashe na ci gaba da yi kira zuwa yan kasar dama yan takara na ganin sun bayar da hadin kai domin gujewa duk wani rikici da kan iya biyo bayan zaben., Kiran dake zuwa bayan da shugabar tawagar ta ‘yan kallo daga Turai Marya Gabriel ta ce tun kafin zaben ne suka fara samun korafe-korafe daga ‘yan siyasa.
Babban Shugaban Yan adawar kasar Gabon Jean Ping na da goyan baya na musaman a kokarin da yake na kawar da shugaba Ali Bongo.
Na baya bayan nan shine janyewar da yan takarar zaben keyi suna mara masa baya.
Na baya bayan nan da ya janye shine Leon-Paul Ngoulakia, wanda dan uwa ne ga Ali Bongo amma ya bayyana goyan bayan sa ga Jean Ping.288