Yayin gudanar da wata zanga zanga jiya Alhamis, wasu daga cikin iyayen sun soki shugaban na Najeriya da karya alkawalin da ya dauka kafin zabe.
Iyayen sun zargi Buhari da fita batun ‘yayansu da ke ci gaba da rayuwa ahannun ‘yan ta’adda.
Daya daga cikin iyayen ‘Yan Matan na Chibok, Enoch Mark, wanda aka sace ‘yayansa biyu ya ce sun zabi Buhari ne saboda alkawarin da ya yi kafin zabe na ceto ‘ya’yansu.
A ranar 14 ga Afrilun 2014 ne Mayakan Boko Haram suka abkawa makarantar garin Chibok suka sace ‘Yan Matan sama da 200.
Daga cikin ‘Yan matan da Boko Haram ta nuna a bidiyon ta bukaci iyayensu su roki gwamnati ta amince da bukatun Boko Haram domin ganin an sake su.
Kungiyar Boko Haram ta bukaci gwamnati ne ta saki mabobinta da ake tsare da su kafin sakin ‘Yan matan na Chibok.288