23 Agusta 2016 - 11:42
Jakadan Siriya A MDD Ya Zargi Kasar Amurka Da Kawayenta Da Ruruta Wutan Yaki A Cikin Kasarsa

Jakadan Kasar Siriya a Majalisar Dikin Duniya ya bayyana cewa: Jiragen saman yakin Amurka suna ci gaba da kashe fararen hula a kasar Siriya musamman mata da kananan yara da sunan kai hare-hare kan 'yan ta'adda.

A jawabin da ya gabatar a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a yayin zaman kwamitin kan binciken mummunan halin da bil-Adama ke ciki a yankin gabas ta tsakiya a jiya Litinin: Jakadan kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ya bayyana cewa: Kasashen da suke da'awar cewa suna son al'ummar Siriya tare da kokarin kare musu yanci; sune kan gaba a fagen murkushe al'ummar kasar saboda hare-haren da jiragen saman yakin Amurka suke ci gaba da kai wa kan kasar ta Siriya da sunan yaki da 'yan ta'adda suna kai wa ne kan gidajen fararen hula lamarin da ke kashe mata da kananan yara.

Ja'afari ya kara da cewa: Wasu kasashe daga cikin kawayen Amurka suke daukan nauyin ayyukan ta'addancin da ake ci gaba da gudanarwa a kasar Siriya, yayin da wasu ke daukan alhakin horas da 'yan ta'addan da ake turawa cikin kasar ta Siriya da nufin aiwatar da hare-haren wuce gona da iri kan fararen hula.

Haka zalika jakadan kasar ta Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya fayyace cewa: Takunkumin da aka kakaba kan kasar ta Siriya yana daga cikin dalilan kara wurga al'ummar kasar cikin mawuyacin hali, kamar yadda hare-haren jiragen saman kawayen Amurka suke kara rusa kasar.288