Rahotanni na cewa wani matashi ne da ba a bayyana adadin shekarunsa ba, ya kwance damarar kayan ababan fashewar da ke dauke da su, a kofar shiga babbar kasuwar garin.
Ana dai bayyana fargabar cewa adadin mutanen da suka mutu ka iya karuwa bisa rashin samun kai daukin gaggawa ga wadanda harin ya rutsa da su.
Harin na ranar Lahadi dai ya faru ne a dai-dai lokacin da jami'an tsaro na Rundunar Hadin Gwiwa a Tafkin Chadi ke ikirarin samun nasarar karya lagon Boko Haram a yankin.288