19 Yuli 2016 - 18:12
SAKAMAKON BINCIKEN  KWAMITIN RIKICIN ZARIYA TSAKANIN SOJOJI DA YAN SHI’A {IMN} YAYI BAZATA. Daga;  Yusuf Sulaiman

SAKAMAKON BINCIKEN KWAMITIN RIKICIN ZARIYA TSAKANIN SOJOJI DA YAN SHI’A {IMN} WANDA KWAMNATIN JIHAR KADUNA TA KAFA YA BADA SAKAMAKON ZAMAN DA YAYI KUMA GA DUKKAN ALAMU RESHE YA JUYE DA MUJIYA.YAYI BAZATA.

Da farko yanda muka kalli Komitin da Gomnatin Kaduna karkashin Gomna Nasiru El-Rufa’a ta kafa domin binciken waqi’ar Zariya mun dauka ba zata yi adalci ba saboda dalilai kaman haka: Wasu daga cikin membobin komitin sun kasance wahabiyawa masu tsananin gaba da kiyayya ga Yan shi’a,har wani ya taba kira da kore yan shi’a daga gidajen haya da kuma sallamar su a wajajen ayyukansu  da sauran nau’o’I na magunta da kuntatawa ga ‘yan shi’a. Wahabiyawa sun so suyi amfani da komitin domin su sanya a haramta aqidantuwa da aqidan shi’a a Nigeriya.Da wannan mugun nufin nasu ne suka dinga gayya daga kusan dukkan sassan kasarnan domin hallara a wannan komitin don gabatar da dukkan nau’I na sharri da suka sani dangane da ‘yan shi’a da shi’anci. A  asali shi komitin an kirkire shi ne-kamar yanda Gomna ya fadi-domin a bincika abinda ya faru da abubuwan da suka haddasa ita waqi’ar ta Zariya ,amma sai komitin ya canja aka koma ana magana akan aqidu na shi’a ko in ce shubhohi da aka jingina su ga ‘yan shi’a. A irin wannan yanayi ne da tsinkaya da hangen nesa da sauke takhlif na shari’a ne Maulana Shaikh Hamzah Muhammad Lawal ya ga ya dace ya hallara a wannan komitin domin ya isar da hakikanin sakon Ahlul Bait da kuma nuna rashin dacewar abin da aka yi na wuce gona da iri ta janibin sojoji akan yan IMN.Wannan ne yasa Shaikh ya aika wa komitin takardan neman izinin zuwa domin ya bada bayani sati biyu bayan kaddamar da komitin. Kafin Shaikh ya bayyana a wannan komiti mutane masu yawa iri na mun shiga cikin damuwa da ganin kamar ba za a taba yi mana adalci ba saboda yanda muka ga bayanai na tafiya a komitin ta fuskoki masu yawa wadanda suke nuna lallai ana so a haramta  shi’anci ne a kasar. A lokacin da Shaikh Hamzah ya je komitin yayi tsokaci akan abubuwa masu yawa wadanda suka dawo dashi Chairman din da komishinonin sa cikin hayyacin su akan lallai fa akwai abubuwan da ya kamata suyi la’akari dasu a wajen wannan bincike.Wanda ya saurari Presentation din Shaikh na san ya fahimci wannan.Shaikh yayi masu bayani akan dalilin kafa komitin da kuma muhimmancin yin adalci da kuma wuce gona da iri da muhimmancin amfani da HEALIN PROCESS da kuma fallasa mugun nufi na wahabiyawa a komitin. Idan ba mu manta ba bayan Presentation din Shaikh duk da an ce akwai memo masu yawa da za a gabatar bayan Shaikh amma sai ya zama komitin ta tashi kowa ya daina zuwa domin bada bahasi wato komitin ya tashi da Presentation din Shaikh. Alhamdulillah a ranar Juma’a da ta gabata ne komitin ya mika sakamakon binciken ga Gomna Nasiru El-Rufa’I kuma yayi alkawari zai bayyana shi kowa ya gani.To yau sai ga shi yau PREMIUM TIMES ta rawaito bangarorin sakamakon binciken-duk da ba duka ta rawaito ba,sai muka ga duk abubuwan da Maulana Shaikh yayi ishara akan su a cikin Presentation din sa an dabbaka su kuma wadanda Shaikh ya zarga da wannan aika aikan na Zariya su aka tuhuma. Muna rokon Allah Ya karawa Shaikh lafiya da kariya da karfin gwiwa a duk lokacin da aka samu irin wannan yanayi mai tsanani.Allah Ya cika masa burinsa. Ga link din da mutum zai karanta rahoton na Premium Times: http://www.premiumtimesng.com/news/headlines/207155-exclusive-judicial-panel-indicts-nigerian-army-general-others-zaria-massacre-shiites.html