19 Yuli 2016 - 17:36
Zaman Tattauna kan Ci Gaban Da Aka Samu Kan Yarejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya

Da safiyar yau ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi tare da tawagarsa suka isa birnin Vienna na kasar Austria, domin halartar tattaunawa kan ci gaba da aka samu a yarjejeniyar shirin nukiliya na kasar Iran.

Tashar talabijin ta kasar Iran ta bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau mataimakin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya isa birnin Vienna na kasar Austria, inda a yau za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin wakilan na Iran da sauran bangarori na manyan kasashen duniya, kan ci gaban da aka samu a yarjejeniyar da aka cimmawa kan shirin Iran na nukiliya, da yadda dukkanin bangarorin suke yin aiki da ita.

A cikin makon da ya gabata ne babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban ki moon ya shirya wani rahoto, wanda a cikinsa yake cewa gwajin makamai masu linzami na ballistic da Iran ta yi ya saba wa wanann yarjejeniya, rahoton da Iran ta ce na siyasa ne kawai, domin kuwa a cikin yarjejeniyar babu inda aka ambaci haka.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin kasar Rasha ta ce wanann rahoto na Ban Kimmon ba ya da tushe, kuam za ta yi fatali da shi matukar dai aka mika shi ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.